Latest
Yan sanda sun kama babban dan daba Gundura da ya fasa motar yan sanda a Kano. Gundura ya fasa motar yan sanda kuma ya jagoranci yan daba a unguwar Dorayi.
Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun shaidawa gwamnatin tarayya rashin jin dadin yadda matsalar lantarki ta girmama a shiyyar ta hanyar samar da karin layukan wuta.
Sheikh Yusuf Musa Assadus Sunnah ya ba gwamnoni shawara kan yadda za a kawo karshen rashin tsaro na ta'addanci inda ya ce ya kamata a soke yan sa-kai.
Shugabanni a Arewacin Najeriya da suka hada gwamnoni da sarakunan gargajiya sun nuna damuwa kan sabon kudiri da ke gaban Majalisar Tarayya na haraji.
Kwamishinan hadin kai da rage radadin fatara a jihar Taraba, Habu James Philip ya jawo cece-kuce a lokacin wani taro a China bayan katobarar da ya yi a furucinsa.
Majalisar dattawa ta fara shirin tantance mutum 7 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin sababbin ministoci bayan ya yi garambawul.
Zakakurin ɗan wasan tsakiya mai taka leda a Manchester City, Rodri ya samu nasarar lashe kyautar ɗan wasa mafi hazaƙa a shekarar 2024 watau Ballon D'Or a Faris.
Matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal ya zama lamba ɗaya a jerin matasna ƴan kwallon da ba su haura shekara 21 ba a duniya, an ba shi kyauta a Faris.
Tsohon shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa watau NDLEA, Fulani Kwajafa ya riga mu gidan gaskiya bayan ƴat gajeruwar rashin lafiya.
Masu zafi
Samu kari