
Latest







Gwamnan jihar Kaduna ya bukaci matasa masu shirin zanga zanga su dakata domin tsoron barkewar rikici a lokacin zanga zanga. Nuhu Bamalli ma ya yi kira ga matasan.

Yayin ya rage saura sa'o'i 48, kungiyoyi da yawa sun sanar da janyewadaga zanga zangar da ake shirin yi kan yunwa da tsadar rayauwa a ƙasar nan a wata mai zuwa.

Kungiyar da ke rajin kawar da talauci da kare hakkin dan Adam a Najeriya da wasu kasashe 45 ta Action Aid ta tunatar da hukumomin muhimmancin tsaro.

Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, matashi da ya goyi bayan zanga-zanga a Najeriya ya rasa rawaninsa na Wakililin matasa a Bosso da ke jihar Niger.

Jam'iyyar NNPP ta yi martani ga dan majalisarta, Kabiru Alhassan Rurum bayan suka da ya yi kan rusa masarautun Kano da Abba Kabir Yusuf ya yi a jihar.

Gwamnatin jihar Sokoto ta raba tallafi Naira Miliyan 10 da tirelolin abinci ga mazauna karamar hukumar Isa da rashin tsaro ya hana su sakewa domin rage radadin.

Fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Muhammad Adamu Dokoro ya soki malaman Musulunci da suka gana da Shugaba Bola Tinubu kan halin kunci.

Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin kirkirar sabuwar sakatariya ta matasa bayan korafin matasa a Abuja inda ya ke ganin hakan zai hana su zanga-zanga.

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa akwai wasu manyan mutane da suke tunzura matasa su fita zanga-zanga don a kifar da gwamnati.
Masu zafi
Samu kari