Latest
Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya shaidawa yan Najeriya kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi domin magance matsalar tattalin arzikin kasa.
Kungiyar Ikoyi Vanguards ta bukaci Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da ya sanya baki kan rigimar sarautar Ikoyi-Ile da ke karamar hukumar Oriire.
Sanata Barau Jibrin ya karbi tsohon hadimin Abba Kabir Yusuf a harkar shari'a zuwa APC. Tarin yan NNPP sun sauya sheƙa a shirin kifar da Abba Kabir Yusuf a 2027.
Yan sanda sun kama babban dan daba Gundura da ya fasa motar yan sanda a Kano. Gundura ya fasa motar yan sanda kuma ya jagoranci yan daba a unguwar Dorayi.
Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun shaidawa gwamnatin tarayya rashin jin dadin yadda matsalar lantarki ta girmama a shiyyar ta hanyar samar da karin layukan wuta.
Sheikh Yusuf Musa Assadus Sunnah ya ba gwamnoni shawara kan yadda za a kawo karshen rashin tsaro na ta'addanci inda ya ce ya kamata a soke yan sa-kai.
Shugabanni a Arewacin Najeriya da suka hada gwamnoni da sarakunan gargajiya sun nuna damuwa kan sabon kudiri da ke gaban Majalisar Tarayya na haraji.
Kwamishinan hadin kai da rage radadin fatara a jihar Taraba, Habu James Philip ya jawo cece-kuce a lokacin wani taro a China bayan katobarar da ya yi a furucinsa.
Majalisar dattawa ta fara shirin tantance mutum 7 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin sababbin ministoci bayan ya yi garambawul.
Masu zafi
Samu kari