
Latest







Jam'iyyar mai mulki a jihar Osun ta gamu da koma baya yayin da wasu mambobi sama da 100 suka jefar da laima, sun koma jam'iyyar APC ranar Lahadi, 21 ga wata.

Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kan jami'an 'yan sanda da ke aikin sintiri a jihar Abia. Miyagun sun hallaka Sufeton 'yan sanda da wasu mutum uku.

Yayin da zaɓen jihar Edo ke kara matsowa, jam'iyyar APC ta roki majalisar dokikin jihar ta gaggauta tsige Gwamna Obaseki kan kalaman da ya yi a bidiyo.

Majalisar wakilai ta dauki matakin shawo kan rikicin da ya barke tsakanin Aliko Dangote da gwamnatin Tinubu wanda hukumar NMDPRA ta koka kan matatar Dangote.

Wani matashi mazaunin jihar Sokoto, Buhari Haruna ya nemi daukin jama'a kan gano wanda ya sace masa injin hada-hadar kudi na POS har wurin sana'arsa.

Jami'ai da ake zargin na farin kaya ne sun cafke wani Bashir Yunusa bayan ya tallata rigar zanga-zangar da ake shiryawa a Najeriya kan yunwa da matsin rayuwa.

Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta yi babban kamu bayan daruruwan mambobin jam'iyyun adawa na PDP, APGA da LP sun dawo cikinta. Sun sha alwashin ba da gudunmawarsu.

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja daga birnin Accra na kasar Ghana, bayan halartar taron koli na tsakiyar shekara karo na 6 na kungiyar Tarayyar Afirka.

An saka 'yar wasan Super Falcons, Asisat Oshoala, da tsohuwar ‘yar wasan Najeriya, Perpetual Nkwocha, cikin jerin ‘yan wasa 25 da suka fi fice a Afirka.
Masu zafi
Samu kari