Latest
Sheikh Ibrahim Ahmad Maqary ya soki tsare ƙananan yara saboda zargin cin amanar ƙasa da kifar da gwamnati. Limamin na ganin alkalai da jami’an tsaro sun yi zalunci
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Isaac Fayose ya musanta zargin da ake yaɗawa cewa ya yi kudi ne lokacin da Ayodele Fayose ke mukin jihar inda ya ce shi ɗan kasuwa ne.
Aliyu Usman Tilde ya kare ministan harkokin ilmi da aka yi waje daga majalisar FEC a watan Oktoba. Idan aka bi ta shi, Farfesa na cikin wadanda suka fi kowa kokari
Wasu miyagu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun je har gona sun kashe manomi da ƴaƴansa guda biyu a yankin karamar hukumar Ivo ta jihar Ebonyi.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ƙaryata labarin kakaba harajin N40,000 ga ma'aikatan jihar da ake yaɗawa bayan fara biyan mafi ƙarancin albashi.
Ministar harkokin mata a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Imaan Sulaiman-Ibrahim ta ziyarci yaran da aka tsare saboda zanga-zangar da aka yi a watan Agusta.
Jam'iyyar APC reshen jihar Bauchi ta yi kira ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta kara himma wajen rage radadin da ake ciki.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daraktan daukar hoto a masana'antar Nollywood da jami'an tsaro suka harba yana cikin mummunan yanayi bayan kai shi asibiti.
Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta bayyana cewa har yanzu ba ta san tsagin da yake da gaskiya ba a rikicin majalisar dokokin jihar Rivers.
Masu zafi
Samu kari