Latest
Chief Abiye Sekibo ya ce Gwamna Fubara ya shawo kan kusoshin Ribas suka juyawa Atiku baya, suka koma layin Tinubu a kokarin da yake na kawo ci gaba a jihar.
Watanni biyar bayan dakatar da ita, hukumar EFCC tana bincikar tsohuwar ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, kan zargin karkatar da kudade har N138m.
Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya ragewa ma'aikata lokacin aiki domin su sami isasshen lokacin zuwa tafsir da yin wasu ibadun a watan Ramadan.
Yayin da ake maganganu kan rufe makarantu a Ramadan, Majalisar shari’ar Musulunci ta goyi bayan matakin a Ramadan, tana cewa hakan zai taimaka wa dalibai.
INEC ta sa wa’adin fidda gwani daga 20 ga Maris zuwa 10 ga Afrilu, ta bukaci jam’iyyu su bi ka’ida don gujewa matsaloli da ka iya hana gudanar da sahihin zabe.
Jami’ar OAU ta shiga alhini bayan Farfesa Jimoh Olanipekun ya yanke jiki ya fadi ana taro. An gaggauta kai shi asibiti, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Sanata Peter Nwaebonyi mai wakiltar Ebonyi ta Arewa a majalisar dattawa ya fito ya yi magana kan takaddamar Sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio.
Majalisar dattawa ta dauki matakan ladabtarwa kan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan samunta da laifin raina shugaban majalisar. An lissafa matakai 6 da aka dauka.
Sanata Natasha Akpoti, dakatacciyar sanatar Kogi ta Tsakiya ta yabi Kayode Fayemi da ya fito ya karyata zargin da wani sanata ya mata na cin zarafi jiya Laraba.
Masu zafi
Samu kari