Latest
Rahotannin da muke samu daga birnin tarayya Abuja ya nuna cewa wata tanka da ta ɗauko iskar da man fetur ya fashe a gadar Karu da ke Abuja, mutane da dama sun rasu.
Ministan shari'a a Najeriya, Lateef Fagbemi ya kare matakin dokar ta-baci da Bola Tinubu ya kafa da cewa ta hana Majalisa tsige Gwamna Fubara daga kan mulki.
Tsohon ɗan takarar majalisar dokokin Kano, Hon. Adnan Mukhtar Tuduk Wada ya soki shugaban matasan PDP na ƙasa, ya ce Muhammad Kadade ya gaza wakiltar matasa.
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya sha alwashin ba Bola Tinubu kuri'u a 2027 yayin da ya karɓi shugabannin kananan hukumomi 17 da suka sauya sheka zuwa APC.
Kujerar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta fara fuskantar barazana a majalisa. Mutanen mazabarta sun fara yunkurin yi mata kiranye domin ta baro majalisa.
‘Yan bindiga sun sace dalibai 2 a jami’ar FUDMA, da ke jihar Katsina yayin da aka ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a Adamawa, an kuma kama malami a Jigawa.
Jarumi a masana'antar Kannywood, Sadik Sani Sadik ya ce yana fim ne ba don koyar da tarbiyya ba, illa neman kuɗi kawai saboda tarbiyya daga gida ake samu.
A karshe, Matatar Alhaji Aliko Dangote ta dakatar da sayar da man fetur da Naira na ɗan lokaci saboda dalilai na musayar kuɗi musamman dalar Amurka.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matakin da aka dauka kan dokar ta baci a jihar Rivers ya yi daidai. Ta fadi makomar kudaden jihar da za a fitar daga asusun tarayya
Masu zafi
Samu kari