Latest
Majalisar wakilan tarayya ta fara tafka muhawar kan bukatar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika mata na ayyana dokar ta ɓaci a jihar Ribas.
Yayin da yan adawa ke kokarin kawo cikas ga mulkin Bola Tinubu a 2027, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan APC sun kafa kawance.
EFCC ta kama Akanta Janar na Bauchi da wasu mutum biyu bisa zargin wawure Naira biliyan 70, yayin da ake binciken Gwamna Bala Mohammed kan lamarin.
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta tabo batun yunkurin yi mata kiranye daga majalisar dattawa. Ta ce ba zai yi tasiri ba.
Manyan 'yan siyasa ba su fara amsa kiran tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i na a hade wuri guda domin fatattakar gwamnatin Bola Tinubu ba.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya roki 'yan Najeriya su tashi tsaye su kare dimokuradiyya daga barazanar dokar ta-baci a Rivers.
Gwamnatin jihar Osun ta bayyana takaicin yadda wasu 'yan APC ke da ra'ayin neman a bayyana dokar ta baci a jihar, kamar yadda Bola Tinubu ya yi a Ribas.
Kamfanin NNPCL ya karyata cewa an kai hari matatar Fatakwal da ke jihar Rivers bayan Tinubu ya dakatar da Gwamna Simi Fubara. NNPCL ya ce matatar na aiki.
Hukumar FAAN ta fara rusa gine-gine a rukunin gidajen ma'aikatan filin jirgin sama da da ke Kano, mazauna wurin sun yi watsi da lamarin, sun nufi kotu.
Masu zafi
Samu kari