Latest
Kunguyar CDD ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Zamfara saboda dalilan karya doka da tattalin arziki.
Yayin da ake shirin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye, INEC ta gudanar da taro kan lamarin bayan fiye da masu zabe 250,000 sun sa hannu kan bukatar hakan.
Malaman firamaren birnin tarayya Abuja sun shiga yajin aiki karo na hudu, saboda gaza biyansu sabon albashi na N70,000. Lamarin ya hana dalibai zana jarabawa.
Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kai ziyara kasuwar Dakata da aka yi gobara, ya ziyarci Sheikh Uwaisu Limanci, Asibitin yara da gidan gajiyayyu.
Jam'iyyar adawa ta NNPP ta bayyana cewa wadanda suka ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu shawarar ya sanya dokar ta ɓaci a Ribas sun karya dokar ƙasa.
Shugaban ma'aikatan jihar Rivers ya yi murabus mako daya bayan dakatar da gwamna Fubara. Ya ajiye aiki ne yayin da aka nada sabon sakataren gwamnatin jihar.
Gwamnatin Kano, karkashin jagorancin Abba Kabr Yusuf ta bayyana takaicin yadda wasu ke kokarin hadda husuma jihar, musamman a kan batun sarauta a jihar.
Yayin da Super Eagles ke shirin wasa a yau Talata, Gwamnatin Akwa Ibom ta sayi tikiti domin rabawa kyauta ga ƴan Najeriya a wasanta da Zimbabwe a filin wasa na Uyo.
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin NiYA a fadar shugaban kasa domin ba matasa horo da samar da ayyuka a Najeriya. An raba miliyoyi wa wasu matasa.
Masu zafi
Samu kari