Latest
Bayan shekaru da dama suna ibada da imani mai karfi ga Ubangiji, wasu ‘yan Najeriya sun yanke shawarar barin addinin Kiristanci bayan bincike da tunani mai zurfi.
Gwamnonin Arewa karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya sun yi Allah-wadai da kisan matafiya a Edo, suna cewa wannan abin takaici ne da ya sabawa doka.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike na adalci kuma a bayyane kan kisan ƴan Arewa a Edo.
Bayan janye hawan sallah da Aminu Ado Bayero ya yi, Sheikh Ibrahim Khalil ya yaba wa basaraken yana mai cewa zaman lafiya ya fi komai muhimmanci.
Tsohon sanatan Bauchi, Suleiman Nazif ya fice daga PDP zuwa SDP don samar da shugabanci na gari. Ya ce matakin ya biyo bayan shawarwari da amincewar mabiyansa.
Jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da kisan matafiya ƴan Arewa da aka ce suna hanyar zuwa Kano a jihar Edo, ya nemi a ɗauki mataki.
Magoya bayan PDP a Filato sun fusata bayan kyautar kayan azumin watan Ramadan da aka ba su, wanda su ke ganin ya yi kadan idan aka kwatanta da hidimarsu ga jam'iyya.
Gwamna Monday Okpebholo ya yi Allah wadai da kisan ƴan Arewa a garin Uromo na jihar Edo, ya ba da umarnin gudanar da bincike don hukunta mau hannu.
Bayan Nasir El-Rufai ya bar APC zuwa SDP, jam'iyyar reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa tsohon gwamna ba mambanta ba ne inda ta ba shi shawara da sauran al'umma.
Masu zafi
Samu kari