Latest
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon ɗan majalisar jihar Legas, Hon. Victor Akande, ya rasu bayan haɗarin mota da ya faru a Ojo makon da ya gabata.
A labarin, za a ji cewa ADC ta ce ta amince da Nasir El-Rufa'i da Peter Obi su ci gaba da zama a jam'iyyunsu yayin da ake shirin babban zaɓen 2027 mai zuwa.
Wani babban jigon APC a Kano, Fa'izu Alfindiƙi ya bayyana shirin da suke yi na tallata shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yadda zai lashe zsɓe cikin sauƙi a 2027.
A labarin nan, za a ji yadda gungun ƴan ta'adda su ka dawo aiki gadan-gadan, inda suke lashe mutane kamar kiyashi a sassan Katsina bayan jama'a sun fara samun sauƙi.
Gwamnati tarayya ta sanar da shirin daukar bayanan manoma da ya hada da sunayen su domin cire masu karbar tallafin bogi. Hakan zai taimaka wajen samar da abinci.
Rikici mai zafi ya kunno kai a jam'iyyar ADC da ƴan adawa suka yi haɗaka a cikinta, tsohon ɗan takarar gwamnan Gombe, Nafi'u Bala ya tada rigima.
'Yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Sokoto bayan sun farmaki manoma. Miyagun sun hallaka manoman da ke tsaka da aiki a cikin gonakinsu a wani kauye.
Kotu a Ilorin ta yanke wa Malam Abdulrahman hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kisan Hafsoh Lawal, ta kuma wanke wasu mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan.
Jarumin Nollywood, Don Richard ya nemi taimako bayan ya sayar da mota don jinya, matarsa ta gudu. An roƙi 'yan Najeriya su taimaka masa da N30m don ya yi magani.
Masu zafi
Samu kari