Latest
Isra'ila ta kai sababbin hare-hare a Lebanon yayin da Donald Trump ya soki matakan Benjamin Netanyahu tare da kira da a rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.
Peter Obi ya bayyana cewa a shirye yake ya mutu saboda Najeriya, yana mai cewa shugabanci na gaskiya na buƙatar sadaukarwa wajen magance matsalar tsaro.
Shugabannin Musulmi da na Katolika a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa domin kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane.
Shahararrun mawaki a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara da Davido sun yi musayar yawu kan matsalar rashin tsaro. Shahararrun mawakan biyu sun zazzagi juna.
Ma'aikatar kudi ta tarayya ta musanta labarin cewa gwamnatin Tinubu na shirin dora karin haraji a harkokin sadarwa da man fetur, ta ce labarin ba gaskiya ba ne.
Wasu mambobin Majalisar Wakilai sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da fifita siyasar zaɓen 2027 kan magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da dimokuraɗiyya.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole ya musanta rahotanni da ke nuna cewa ya yi zargin an yi sa hannun sanatoci na bogi a rahoton dakatar da Natasha.
Kungiyoyin NLC da TUC sun sanar da shirin fara tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi, saboda hauhawar farashi da ta yi wa ma’aikata katutu.
Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta yi murabus. Mataimakin shugaban kasar ya sanar da cewa gwamnatin ta yi murabus kan rashin yin abin a zo a gani.
Masu zafi
Samu kari