Latest
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun tafka babban kuskure ta hanyar sake zaben jam'iyyar APC a 2023.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga kungiyoyin kwagadon NLC da TUC kan tafiya yajin aiki a gobe Litinin. Ministan yada labarai, Idris Muhammad ne ya yi kiran.
A ci gaba da tsaftace kafafen sada zumunta da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta soma, ta sake cafke dan TikTok din nan Rabi'u Sulaiman, da aka fi sani da Lawancy.
Kwana nan Aminu Ado Bayero ya kai ziyara wajen Sarkin Ijebu Ode a jihar Ogun a lokacin ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya nada Muhammadu Sanusi II.
Mutane da dama a Kano sun fara shiga fargaba kan yawaitar ƴan daba a fadin jihar musamman saboda rigimar sarauta da ake yi inda suka bukaci karin jami'an tsaro.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mawakin nan kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh saboda zargin yi wa Alkur’ani Mai Girma Izgili da kuma yin kalaman batsa.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya zayyana sunayen wa wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati da zai katse wutar su saboda rashin biyan kudin wutar.
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da dakile harin ƴan daba da suka yi yunkurin kai hari gidan shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Abbas a ranar Juma'a.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa bai yi nadama ba kan mika mulkin da ya yi a hannun farar hula ba a kasar nan.
Masu zafi
Samu kari