Latest
Jam'iyyar NNPP ta ce ta gano yadda jam'iyyar APC ke dauke da alhakin rura rikici a sauran jam'iyyun kasar nan saboda cimma bukatun kashin kai a zaben 2027.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi wa yan kwadago sababbin alkawura kan karin kudin fetur. Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tabbatar an yi karin albashi a dukkan jihohi.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya yi kira ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya sake tunani kan manufofinta na tattalin arziki, ya ce mutane na cikin wahala.
Wata mota mai amfani da iskar gas na CNG ta fashe a wani gidan mai da ke jihar Edo. Lamarin ya jawo firgici yayin da wasu mutane suka samu raunuka.
Tsohon Ministan yada labarai, Jerry Gana ya yi jimamin mutuwar Sanata a Najeriya, Jonathan Zwingina wanda ya rasu a farkon watan Oktoban 2024 da ta gabata.
Gwamnatin tarayya ta ce dole a cigaba da samun matsalar wutar lantarki a fadin kasar nan, saboda wasu dalilai da su ka hada da lalacewar kayan lantarki.
Dan majalisa mai wakiƙtar Minjibir, Abdulhamid Abdul ya tabbatarwa hukumar Hisbah cewa nan ba da jimawa ba za a kara masu albashi da alawus alawus.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya bayyana cewa hakurin da Shugaba Tinubu ya ba shi ya sanya ya ki barin Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ya isa Sweden domin wakiltar Bola Ahmed Tinubu. Kashim Shettima zai tattauna ne kan harkokin kasuwanci.
Masu zafi
Samu kari