Latest
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bar PDP ya koma APC, inda ya shiga kara jerin gwamnonin da suka fice daga jam’iyyar tun bayan zaben 2023.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya damu zama ɗan takarar gwamnan jihar Kwanaki kadan bayan ya sanar da sauya sheka daga PDP.
An bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar Accord, hakan na zuwa ne awanni bayan ya yanki kati.
Yankin Yarbawa sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi da hukuncin kisa ga masu garkuwa, domin magance hare-haren yan bindiga da rikice-rikicen tsaro a Najeriya.
Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, a yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matakan da ya dauka saboda rashin tsaro.
Jam'iyyar PRP ta bayyana cewa ba ta da wurin da za ta karbi Gwamna Bala Mohammed ko da rahoton da ake yadawa gaskiya ne, ta ce ya illata jihar Bauchi.
A labarin nan, za a ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana rashin jin dadi gane da shawarar da Siminalayi Fubara ya yanke na komawa APC, ta ce ya nuna rauni.
Tsohon kwamishinan Kano, Muaz Magaji ya soki shirin kasa sabuwar Hisbah da Abdullahi Ganduje ke shirin yi a Kano. Ya ce Ganduje zai kawo fitina a Kano da Arewa.
Kungiyoyin matasan Arewa a jihar Kano sun soki yunkurin kafa sabuwar Hisbah da za ta dauki jami’an da aka sallama, suna cewa hakan barazana ne ga doka.
Masu zafi
Samu kari