Latest
Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya wadatar da sababbin takardun Naira tare da fara janye tsofaffin gabanin 31 ga watan Disambar 2024.
Sojojin Najeriya sun kama jagoran da ya kafa kungiyar ta'addanci ta ESAN a Imo. Sojojin sun kuma wasu manyan yan ta'addan IPOB a Kudancin Najeriya tare da makamansa.
Tsohon shugaban hukumar zabe a Najeriya, Farfesa Humphrey Nwosu ya riga mu gidan gaskiya a birnin Virginia da ke Amurka yana da shekaru 83 a duniya.
Karamin ministan albarkatun man fetur (gas), Ekperipke Ekpo, ya bayyana kudurin Tinubu na fadada amfani da CNG, wanda ya bayyana a matsayin mafi aminci da araha.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura wasika ga majalisar dattawa domin tantance ministocin da ya zaɓo. A ranar Laraba majalisar dattawa za ta tantance ministocin.
Masu ruwa da tsaki na PDP a shiyyar Arewa ta Tsakiya sun fara zaman tattaunawa domin lalubo wanda za su gabatar a matsayin wanda zai maye gurbin Damagum.
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne sun kai hari kan wasu mutane a kusa da jami'ar UNIZIƘ a jihar Anambra. Ana fargabar sun hallaka mutane shida.
Gwamnatin Najeriya ta ce ba dole sai kasashe sun rika daukar shawarwarin Asusun bayar da lamuni da sauran manyan hukumomin duniya ba domin ta gwada hakan.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da shirinta na kara harajin VAT da yan kasar nan su ke biya kan kayayykin da su ke saye ko sayarwa ga yan Najeriya.
Masu zafi
Samu kari