Latest
Bobrisky ya isa iyakokin Najeriya da ke Seme tsakar dare sai aka kama shi. An binciki Bobrisky har zuwa karfe 4:00 na yamma kafin a kawo shi Legas.
Gwamnatin tarayya ta bakin ministan tsaro ta bayyana cewa ba za tattauna da 'yan bindiga ba. Ministan ya ce za a ci gaba da fatattakar miyagun a kasar nan.
'Yan wasan Kano Pillars (U-19) sun yi hatsarin mota a kan hanyarsu ta zuwa sabon filin wasanni na Jos. An ce direban motar da 'yan wasa da dama sun jikkata.
Majalisar dattawan Najeriya ta kafa kwamitin da zai binciki zargin da hukumar NDLEA ke yi wa Sanata Oyelola Yisa Ashiru na samun kwayoyi a gidansa.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP ta kara faɗawa cikim rigima yayin da tsagin Gwamna Bala Mohammed ya maka ƙara a gaban kotun kan taron NEC.
Mummunar ambaliyar ruwa ta jefa ƙauyuka sama da 50. Babbar gadar da ta haɗa kauyuka ta rushe bayan an kwana biyu ana tafka ruwan sama mai karfi gaske.
A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da taron kasa kan dakile aikata laifuffuka ta yanar gizo wanda hukumar EFCC ta shirya a dakin taro na fadar shugaban kasa.
Gwamnatin jihar Abia ta shirya fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N70,000. Gwamnatin za ta fara biyan albashin a watan Oktoba.
Majalisar kasa wakilan kasar nan ta gaji da yawaitar garkuwa da mutane da miyagun yan ta'adda ke yi a babbar birnin tarayya Abuja a kwanakin nan.
Masu zafi
Samu kari