Latest
Kungiyar gwamnonin APC ta ce babu dalilin yin zanga-zanga a dai-dai wannan lokaci inda ta ce ba ta san musabbabin hakan ba tare da kiran a zauna a teburin sulhu.
Matasan kasar nan da sauran masu shirin fita zanga-zanga sun kara samun karfin gwiwa daga tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Faduri Oluwadare Joseph.
An samu asarar rayukan mutum hudu bayan wani gini ya rufto musu a jihar Legas. Hukumomi sun samu nasarar ceto mutum biyar da lamarin ya ritsa da su.
Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da dasa bishiyoyi miliyan 3 a fadin jihar Kano domin inganta noma, yaki da zaizayar kasa da dumamar yanayi a fadin jihar Kano.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta ba da umarnin korar shugaban yaki da cin hanci a jihar, Muhuyi Magaji Rimingado saboda saba umarnin kotu.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojoji ba za su zuba hannu suna kallo a tayar da tarzoma kamar tashin tsahinar da tabfaru a ƙasar Kenya ba.
Kungiyar direbobin tankar mai ta kasa wacce ke karkashin kungiyar ma'aikatan man fetur da iskar gas ta ce babu wani daga cikin mambobinta da zai shiga zanga-zanga.
Gwamnatin Legas ta bayyana fargabar masu zanga-zanga za su iya jawo tashe-tashen hankula da zai salwantar da rayuka da dukiyoyin mazauna cikinta.
Gwamnatin jihar Bauchi ta fito ta bayyana cewa babu wata zanga-zangar da za a gudanar a fadin jihar. Ta gargadi masu shirin yi da su tafi wani waje ba Bauchi ba.
Masu zafi
Samu kari