Latest
Fadar shugaban kasa ta fito ta musanta batun wani jawabi da ake cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi inda ya dauki matakan tsuke aljihun gwamnati.
Wasu mayakan Boko Haram ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke Konduga a jihar Borno inda suka kashe jami'ai, sace makamai da kona motoci.
Gamayyar sarakunan gargajiya a Kudu maso Gabashin Najeriya sun roki Shugaba Bola Tinubu alfarmar samar da sababbin jihohi a yankin da suke da guda biyar.
Karamin ministan albarkatun ruwa, Bello Goronyo, ya jaddada cewa gwamnatin Bola Tinubu na aiki tukuru domin gyara tattalin arziki, ya roki a karawa Tinubu lokaci.
Wani tsohon soja a Najeriya ya bayyana yadda ya ji bayan ya kammala aiki a Najeriya, inda yace da ma a Namibia aka haife shi ba a Najeriya ba. Ya bayyana dalilinsa.
Jam'iyyar APC ta ci karo da cikas da daruruwan magoya bayanta da na LP suka watsar da jam'iyyunsu inda suka da koma PDP a jihar Edo ana shirin zabe.
Wasu jagororin jam'iyyar APC a jihar Cross Rivers sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar mai mulki a jihar. Sun tattara kayansu zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.
Matasan Najeriya sun fara nuna goyon bayansu ga Dangote a kafar sada zumunta ta Twitter tun bayan da aka bayyana fara rikici tsakanin Dangote da wasu jami'ai.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana karancin mai a halin yanzu yayin da gidajen mai suka daidaita farashin man.
Masu zafi
Samu kari