Latest
Allah ya yi wa tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Hon Christopher Ayeni rasuwa sakamakon wani mummunan hatsari da ya rutsa da shi.
'Yan bindiga sun yi yunkurin kai harin ta'addanci a jihar Plateau. Jami'an tsaro na 'yan banga sun yi musayar wuta da su wanda hakan ya jawo asarar rayuka.
Tsohon Minista, Sunday Dare ya fadi wanda ya yi sanadin samun shugabancin kasa da Muhammadu Buhari ya yi inda ya ce Bola Tinubu ne ya yi komai a zaben.
Jami’an hukumar kwastam ta kasa sun yi nasarar raba Najeriya da fetur da ya kai N71,760,930 idan ya shiga kasuwa, an yi kamen ana shirin sa ta a mukamin.
Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi tir da yadda matsalar man fetur ta ƙi ci ta ƙi cinyewa bayan albarkar mai da ke danƙare a ƙasar, kuma su na ganin haka bai dace ba.
Ministan wuta ya buƙaci jihohin Arewa su samar da wuta domin kaucewa shiga duhu. Hakan na cikin shirinTinubu na rage matsalar lantarki a Arewacin Najeriya.
Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa zuwa yanzu mutane miliyam 25 sun samu tallafin rage raɗaɗi kowane N25,000 a sassan Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya yi martani ga gwamnonin Arewa bayan sun fara yaƙar tsarinsa da yake shirin kawowa na karɓar haraji a fadin Najeriya yayin wani taro a Kaduna.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta yi caraf da wani karamin yaro ɗan shekara 16, Nuhu Haruna, bisa zargin kashe abokiyar zaman mahaifiyarsas a Dutsinma.
Masu zafi
Samu kari