Latest
Tsohon dogarin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya bayyana hakikanin makiyan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kasar nan.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammeda ya ce babu wani abu mai ma'ana da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya faɗa a jawabin da ya yi kan zanga zangar da ake yi.
Yayin da aka tafka barna a Kano yayin zanga-zanga, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya koka kan rawar da jami'an tsaro suka taka kafin faruwar hakan a jihar.
Majalisar wakilai ta fito ta gayawa duniya hakikanin albashin da ake biyan 'yan majalisar duk wata. Majalisar ta ce N900,000 da ake yadawa ba gaskiya ba ne.
Kungiyar Kano Progressive Movement ta yabawa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kan kokarinsa lokacin zanga-zanga wurin samar da zaman lafiya a jihar.
Hukumar da ke kula da harkokin matasa masu yiwa ƙasa hidima a Najeriya NYSC ta ayyana ɓatan kodinetan da ke kula da jihar Akwa Ibom tare da direbansa.
Babban daraktan hukumar NPC, Baffa Dan Agundi ya bayyana shirin ma'aikatarsa wurin samar da ayyukan yi har miliyan daya a Najeriya da samar da kudin shiga N3bn.
Gwamnatin jihar Zamfara ta karyata cewa ta ware kudi ₦19.3bn ga kayan dafa abinci a jihar. Gwamna dauda Lawal ya bayyana cewa ₦400m aka ware ga aikin.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su kara hakuri kan wuyar da suke sha sakamakon manufofin da ya kawo a gwamnatinsa. Ya ce sauki na tafe.
Masu zafi
Samu kari