Latest
Gwamma Douye Diri na jihar Bayelsa ya bai wa ma'aikatan gwamnati hutu daga ranar 24 ga watan Disamba, 2024 zuwa 30 ga wata, ya taya su murnar kirismeti.
NNPC ya ce tsohuwar matatar Fatakwal na aiki, tana samar da man fetur da dizel, bayan gyaran dala biliyan 1.5; kamfanin ya roki jama'a su daina yarda da jita jita.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar yara bakwai da wasu mutane uku yayin turereniya domin samun kayan tallafi saboda halin kunci a wani coci a Abuja.
Domin rage zaman kashe wando, gwamnan jihar Akwa Ibom ya raba jalin N50,000 ga matasa akalla 15,000 a faɗin kananan hukumomi 31, ya ce zai faɗaɗa shirin.
Hukumomi a kasar Nijar sun zargi Najeriya da Bola Tinubu da neman kawo cikas a mulkin sojoji a kasar inda ta ce yana hada baki da wasu ƙasashen duniya.
Ado Gwanja ya saki kundin wakoki mai taken Dama Nine wanda ya ƙunshi sababbin wakoki 18, yanzu ana iya sauraron su a YouTube, Audio Mack da Apple Music.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa ya amince da gina filin jirgin saman kasa da ƙasa ne domin ta haka ne kaɗai masu zuba jari za su zo jihar.
Kotun Abuja ta tsare Olamide Thomas kan tuhume-tuhume uku da suka shafi barazana ga dan shugaban kasa. An dage shari’ar zuwa 30 ga Disamba don ci gaba.
Tsofaffin shugabannin kasa a Najeriya za su samu N27bn a shekarar 2025 da aka ware domin biyansu hakkokinsu tare da mataimakansu lokacin mulkinsu.
Masu zafi
Samu kari