
Labaran Kannywood







Jarumar Kannywood, Maryam Malika, ta runtuma kotun Shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna domin neman a tabbatar da sakin da tsohon mijinta mai suna Umar ya yi mata.

Kamfanin man Najeriya na NNPCL ya shirya hadaka da jaruman Kannywood kan wayar da kan 'yan kasa. Ya zauna da Rahama Sadau, Hadiza Gabon da sauransu.

Masana'antar Nollywood ta shiga yanayin alhini sakamakon mutuwar fitacciyar jaruma, Pat Ugwu, ta mutu tana da shekara 35 a duniya, jarumao sun fata ta'aziyya.

Jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Arewa watau Kannywood, Maryam Yahaya ta sayi sabuwar mota kirar Marsandi Benz, mutane sun taya ta murna.

Bayan kalaman Usman Soja Boy kan shirya fina-finai a masana'antar Kannywood, furodusa Abdulaziz Dan Small ya kalubalanci mawakin kan alfaharin da ya yi.

Masu kallo sun roƙi a cire Firdausi Yahaya daga shirin Jamilun Jiddan, duk da haka ta zama fitacciya a fina-finai da ta samu kambun "Jaruma Mai Tasowa."

Usman Soja Boy ya ce Kannywood ba ta tsinana masa komai ba. Ya yi zargin shi ne ke taimakawa masana’antar, kuma dakatarwar ba za ta wani dame shi ba.

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ba za ta lamunci rashin tarbiyya da take dokokin addinin Musulunci da wasu 'yan Kannywood ke yi da sunan sana'a ba.

Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar jarumi Yaya Ɗanƙwambo, an yi mata sutura a Samarun Zaria. Haka zalika, Mahaifin jarumi Baba Ari ya rasu, kuma an yi masa sutura.
Labaran Kannywood
Samu kari