Labaran duniya
Wasu fisatattun matasa sun cinnawa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wuta a jihar Benue. Matasan dai na yin zanga-zanga ne kan matsalar tsaro.
An samu asarar rayuka bayan aukuwar turmutsitsi a wurin wani taron addini a kasar Indiya. Da yawa daga cikin mutanen da suka rasa ransu mata ne da yara.
Hukumomi a kasashen Larabawa da dama sun dauki mataki yayin da ake ci gaba da fuskantar zafi a yankin inda suka rage lokutan sallar Juma'a zuwa wasu mintuna.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da rasuwar wasu mahajjatan Najeriya da dama yayin aikin hajjin bana na shekarar 2024 da muke ciki daga jihohi daban-daban.
Hukumar NAHCON ta jinjinawa mahajjaci mai suna Muhammad Na'Allah daga yankin Gummi a jihar Zamfara da ya mayar da kudin tsintuwa da suka kai €1,750.
Wani harin kwanton bauna da wasu ‘yan ta’adda suka kai a Jamhuriyar Nijar ya yi sanadin mutuwar sojoji 21 a kusa da iyakar kasar da Burkina Faso a ranar Talata.
Kasar Saudiyya ta amince da nadin Sheikh Abdulwahab Al-Shaibi a matsayin sabon mai rike makullin ɗakin Ka'aba. Shi ne na 110 a tarihin masu rike makullin
Allah ya yi wa mahaifiyar mahaifiyar fitaccen dan wasan kwallon kafa na Brazil, Pele, Celeste Arantes rasuwa tana da shekara 101. Ta rasu a ranar Juma'a a Brazil.
Saleh Al-Shaibi ne na 109 cikin wadanda suka rike makullin Ka'aba tun daga kan sahabi Usman Bin Dalha. Yan kabilar Shaibah ne ke rike da makullin a tsawon tarihi.
Labaran duniya
Samu kari