Labaran duniya
Hezbollah ta sanar da sabon Sakatare Janar, Naim Qassem da zai jagorance ta bayan kisan tsohon shugaban kungiyar, Hassan Nasrallah da Isra'ila ta yi.
Da yake amfani da gogewa a harkar fina-finai, talabijin, kiɗa, da ƙwallon ƙafa, ɗan fim ɗin ya ce ya kulla jarjejeniya da gwamnatin Katsina domin horar da matasa.
Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare kan kasar Iran a cikin tsakar dare. Iran ta ce hare-haren ba su yi wata barna mai yawa ba yayin da Amurka tace tana sane.
IMF ya ce babu ruwansa a cire tallafin fetur a Najeriya. Daraktan Afrika na asusun, Abebe Selassie ne ya fadi haka, ya ce amma mataki ne mai kyawun gaske.
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ba zai wakilci Najeriya a taron kasashen Commonwealth na 2024 da za a yi a Samoa kamar yadda aka tsara tun farko ba.
Kasar Amurka ta bayyana cewa lokaci ya yi da Isra'ila za ta tsagaita wuta tare da kawo karshen kashe Falasdinawa da ke zaune a Zirin Gaza da aka shekara ana yi.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai da ba a san ko su wanene ba sun hallaka dan takarar shugaban kasa a kasar Mozambique. Sun kuma hallaka lauyan 'yan adawa.
Majalisar dattawan Kenya ta kada kuri'ar tsige mataimakin shugaban kasar, Rigathi Gachagua kan cin hanci da rashawa da wasu tuhume tuhume 10 da ya musanta.
Bankin duniya ya ba Tinubu shara kan kar ya kuskura ya dawo da tallafin man fetur da farfado da darajar Naira wanda su ne tsare tsaren shugaba Bola Tinubu.
Labaran duniya
Samu kari