Labaran duniya
Wani dan Najeriya ya shiga hannun yan sanda a kasar Burtaniya bayan ya salwantar da ran matarsa wacce suka kwashe shekara 17 suna rayuwar aure tare.
Shugaban kasar Guinea Bissau ya rufe Majalisa ganin Sojoji sun nemi ‘hambarar’ da gwamnatinsa. Mai girma Umaro Sissoco Embalo ya ce sojoji sun shirya kifar da shi.
A cewar asibitin a shafin Facebook sun yi amfani da fasahar IVF akan dattijuwar, kuma tana cikin koshin lafiya bayan haihuwar. Dattijuwar ta kafa tarihi a Afrika.
Dokin zuciya ya ja wani ango ya kashe amaryarsa, kanwarta da surukarsa a ranar aurensu a lardin Arewa maso Yammacin kasar Thailand. Ya kuma harbi wasu hudu.
An samu fargabar yin juyin mulki a kasar Saliyo lokacin da wasu yan bindiga suka kai farmaki a wani barikin sojoji tare da kokarin kwace wajen ajiyar makamai.
Majalisar kungiyar ECOWAS ta yi kira ga gwamnatoci da shugabannin kasashe su duba yiwuwar janye takunkumin da suka kakabawa kasar Nijar bayan hambare Bazoum.
Matasan sun gamu da ajalinsu ne a wajen tantance su a wani shiri da hukumar sojin kasar ke yi na daukar matasa 1,500 aiki, lamarin da ya jikkata mutane da dama
Allah ya karbi rayuwar mai kula da kabari da kuma dakin Manzon Allah (SAW), Abdou Ali Idris a jiya Litinin 20 ga watan Nuwamba, ya na daga cikin masu kula masallaci.
Gwamnatin kasar Mawali ta yanke hukuncin dakatar da shugaban kasa da mukarrabansa daga duk wasu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje. Shugaban kasar ya dau wannan mataki
Labaran duniya
Samu kari