Labaran duniya
Azumin Ramadan na farawa daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana, kuma yana ɗaukar daga sa'o'i 12 zuwa 17, ya danganta da inda mutum ya ke rayuwa a duniya.
Elon Musk, mai kamfanin X ya yi martani bayan daukewar shafukan Facebook da Instagram inda ya ce su kam shafinsa na tafiya yadda ya kamata ba kamar na Zuckerberg ba.
Bayan ɗage dukkanin takunkumi da kungiyar ECOWAS ta ƙaƙabawa kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, an ci gaba da kai wuta Nijar, mazauna kasar sun yi martani.
Yayin da ake fama da yunwa a Najeriya, kasar Ukraine ya farantawa 'yan kasar rai bayan ba da tallafin hatsi tan dubu 25 don rage matsalar yunwa da ake ciki.
Madugun 'yan adawa na kasar Chadi, Yaya Dillo Djerou, ya rasa ransa yayin da sojoji suka kai farmaki a hedikwatar jam'iyyarsa kan zargin yunkurin juyin mulki.
Shugaban kasar Aljeriya ya kaddamar da wani katafaren masallaci a gabar tekun 'Bahar Rum' wanda ya zama mafi girma a Afrika kuma na uku mafi girma a duniya.
Wani jami'in sojan sama na kasar Amurka ya cinna wa kansa wuta domin nuna adawa da kisan kare dangin da kasar Isra'ila take yi wa al'ummar Falasdinawa.
Binciken da Legit Hausa ta yi a shafin yanar gizon ECOWAS ya nuna cewa har yanzu kasashen uku na cikin jerin sunayen mambobin kungiyar, yanzu sun koma 15.
Kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ke yi wa jagoranci ta janye takunkumin da ta dora wa Nijar.
Labaran duniya
Samu kari