Labaran duniya
Masu shirya gasar Miss Universe sun musanta rahotannin da ke cewa Saudiyya na shirin shiga gasar a karon farko, kenan sun karyata ikirarin da Rumy Alqahtani ta yi.
Dattijon da ya fi kowa shekaru a duniya, Juna Vicente Perez Mora ya rasu a jiya Talata 2 ga watan Afrilu da shekaru 114 a kasar Venezuela bayan fama da jinya.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gamu da mummunan hatsarin mota inda ya ci karo da wani direban babbar mota a jiya Alhamis a ƙasar.
Yayin da ake shan fama a wannan wata na Ramadan, Gidauniyar Sarki Salman ibn AbdulAziz ta raba kayan abinci ga gidaje 2,000 a kananan hukumomi takwas a Kano.
An sanar da Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zaben kasar Senegal inda ya kafa tarihi a matsayin matashi mafi karancin shekaru a zaben da aka gudanar.
Dan siyasar Senegal mai shekaru 44, Bassirou Diomaye Faye, ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a nahiyar Afirka. Ya samu kuri'u mafi rinjaye.
Wani sojan ruwa Amurka wanda haifaffen Najeriya ne ya gamu da ajalinsa a cikin tekun Bahar Maliya. Sojan ya yi bankwana da duniya ne bayan ya fada cikin ruwa.
Akwai yiwuwar Falasdinawa su samu sakin mara bayan da kasashen Turai suka bayyana amincewarsu a ba kasar 'yancin kai cikakke don kawo mafita ga rikici.
Kasar Saudiyya ta cika alkawarin da ta dauka a watan Janairu cewa za ta buɗe wasu shagunan kwankwadar barasa a birnin Riyadh domin baki 'yan kasashen waje.
Labaran duniya
Samu kari