Rasha ta rasa 40% na Dakarun Sojojin da ta aika su aukawa mutanen Ukraine inji Jami’i
- Ana tunanin kasar Rasha ta rasa kimanin 40% na duk sojojinta da ta aika domin su yaki Ukraine
- Bayanai su na nuna cewa kusan rabin sojojin Rasha sun hallaka, ko kuma sun yi asarar makamai
- Rahotanni sun tabbatar da cewa sojoji su na nan a Mariupol, sun hana a kai wa Ukraniyawa agaji
Ukraine - Rahotanni daga kasar Ukraine sun bayyana cewa Rasha ta rasa abin da ya kai 40% na sojojinta da su ka burmawa Ukraine a yakin da ake yi.
A ranar Laraba Euromaidanpress ta rahoto cewa makonni uku da soma wannan yaki, sojojin Rasha su na fuskantar kalubale saboda yanayin Ukraine.
Hakan ya jawo Rasha ta rasa kusan rabin adadin sojojin da ke yakar makwabciyarta. Ko dai an hallaka dakarun kasar, ko kuma sun rasa kayan yakinsu.
A daidai wannan lokaci kuma sojojin na Rasha sun jawowa kasar Ukraine asarar kimanin Dala biliyan 565 daga karshen watan Fubrairun zuwa yanzu.
Har ila yau, ana zargin sojojin Rasha sun ruguza gidajen mutane kusan 2700, sannan sun kashe kananan yara 97 da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
An samu wadannan alkaluma ne daga rahotannin yanar gizo, bayanan jami’ai da tattaunawa ko binciken da masana suka gudanar a ‘yan makonnin nan.
Jaridar Vanguard ta ce jami’in da ya bada lissafin sojojin Rasha da aka yi illa, bai tantance adadi ba. Har yanzu ba a iya tabbatar da gaskiyar alkaluman ba.
'Yan Mariupol sun ga ta kansu
Mutanen da ke zaune a yankin Mariupol su na cigaba da fuskantar matsanancin barazana. A duk rana sai an hallaka mutanen Ukraine da-dama a wannan gari.
Kamar yadda mu ka samu labari, sojojin Rasha su na kokarin rufe wannan babban gari wanda yake kusa da Kiev, amma kasar ta na ta asarar sojoji a yunkurin.
An hana bada agaji - Volodymyr Zelensky
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce an yi kokarin kai kayan agaji ga mazauna kewayen Mariupol, amma sojojin Rasha sun hana a kai agaji.
Gwamnatin Ukraine ta tabbatar da cewa sama da mutane 20, 000 sun tsere daga Mariupol ta Ruwan Azov.
A halin yanzu kasashen makwabta; Poland, Czech Republic da Slovenia sun sa baki a rikicin na Ukraine da Rasha domin ganin an kawo karshen wannan masifa.
Sojoji nawa aka kashe?
A kwanakin baya kun ji cewa Kasar Rasha ta ce sojojinta 500 suka hallaka. Amma gwamnatin Ukraine ta ce ta kashewa Rasha dakaru sama da 12, 000 a kwanaki 12.
Ministan harkokin kasar wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya bayyana cewa Rashawa sun hallaka Bayin Allah 1500 a garin Mariupol, daga ciki watakila har da da yara.
Asali: Legit.ng