Labarai Kai tsaye kan Yakin Rasha-Ukraine: Rasha da Ukraine sun yi Yarjejeniya kan Fitar da Kayan Hatsi
A ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, kasar Rasha ta fara kai hare-hare cikin Ukraine da nufin kwace kasar daga hannun Vlodomyr Zelensky, Shugaban kasar
- Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa kasarsa ta hakura da shiga cikin kungiyar NATO
- Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi kira ga Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya zauna suyi magana
- Gwamnatin Amurka na bada shawarar kasashe su daina sayan man feturin Rasha
Da yiwuwan a samu saukin farashin kayan masarufi, Rasha da Ukraine sun yi yarjejeniya kan fitar da kayan hatsi
Biyo bayan hauhawar farashin kayan hatsi a fadin duniya, da yiwuwan a samu saukin farashin kayan masarufi, Rasha da Ukraine sun yi yarjejeniya kan fitar da kayan hatsi.
Kasar Rasha da Ukraine sun rattafa hannun kan sabuwar yarjejniya da kasar Turkiyya da Majalisar dinkin duniya kan fitar da kayan hatsi da ake bukata a fadin duniya.
Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa an yi wannan yarjejeniya ne ranar Juma'a.
Wannan yarjejeniya zai baiwa kasar Ukraine damar fitar da kayan hatsi sauran kasashen duniya tun bayan hanasu da Sojoji Rasha suka yi.
Ministan tsaron Rasha, Sergei Shoigu da Ministan ayyukan Ukraine Oleksandr Kubrakov, sun rattafa hannu kan yarjejeniyar lokuta daban-daban da Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres da Ministan tsaron Turkiyya, Hulusi Akar.
Dirakta janar na kungiyar agaji, Red Cross, Robert Mardini, yace a watanni shida da suka shude, farashin kayan masarufi sun hau ninkin ba-ninki a wasu kasashen duniya.
A cewarsa, farashi sun tashi 187% a Sudan, 86% a Syria, 60% a Yemen da 54% a Ethiopia.
Yace:
"Yarjejeniyar da zata ari a fitar da kayan hatsi da bakin teku ba karamin taimakon al'ummar duniya dake fama da yunwa zata yi ba."
Rasha ta kwace garin Lyman
Hukumar Sojin Rasha ta bayyana cewa ta kwace garin Lyman dake gabashin Ukraine yayinda take cigaba da kokarin kwace birnin tarayyar kasar.
Ma'aikatar tsaron Rasha a jawabin da ta saki tace:
"Sakamakon hadin kan dakarun jamhuriyyar Donestks da Sojin Rasha, mun kwace birnin Lyman daga hannun yan Ukraine."
Mun saduda, muna hakura da shiga kungiyar NATO: Shugaban kasar Ukraine
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky , a ranar Talata ya bayyana cewa kasarsa ta hakura da shiga cikin kungiyar NATO, babban dalilin da yasa Rasha ta fara yakin nan.
A hirar da yayi da rundunar Sojin gaggawa karkashin Birtaniya, Zelensky yace da alamun zasu hakura tunda an fada musu ba zasu iya shiga ba, rahoton Aljazeera.
Instagram ya daina aiki a Rasha
Instagram ya daina aiki Rasha bayan gwamnatin kasar ta tukunci kamfanin Meta da bari mutane na kira ga a hallaka yan kasar.
Wannan na zuwa ne bayan hana amfani da Facebook da Tuwita a farkon watan nan da gwamnatin Rasha tayi don hana yan kasar ganin abubuwan dake gudana a Ukraine.
Instagram ta shiga jerin shafukan yanar gizon da hukumar Roskomnadzor ta sanyawa takunkumi, rahoton Aljazeera.
An kashe mutum sama da 2,500 a Mariupol, hadimin shugaban Ukraine
Sama da mutum 2,500 mazauna garin Mariupol suka rasa raykansu tun lokacin aka fara yakin Rasha da Ukraine, hadimin shugaban kasar, Oleksiy Arestovych, ya bayyana hakan.
Ya ce wannan shine adadin da mahukuntan garin Mariupol suka bada.
An kammala zaman sulhu tsakanin Ukraine da Rasha a Turkiyya, ba'a cimma komai ba
Gwamnatin kasar Turkiyya ta shirya zaman sulhu tsakanin Ministocin harkokin wajen Rasha da Ukraine a birnin Antalya ranar Alhamis.
Babban hadimin Zelensky ya ce Ukraine ta yi asarar dukiyar $100bn kawo yanzu
Mai baiwa shugaban kasar Ukraine shawara kan tattalin arziki, Oleg Ustenko, ya bayyana cewa kawo yanzu an yiwa kasar asarar dukiya, gine-gine da sauransu na akalla $100bn.
Oleg Ustenko ya bayyana hakan a wani taron yanar gizo da cibiyar tattalin arzikin duniya na Peterson Institute ta shirya.
Ya ce kashi 50 cikin 100 da kasuwannin Ukraine a rufe suke, yayinda sauran ke aiki cikin dar-dar.
Karya ne, bamu kai hari asibitin yara ba - Rasha
Kasar Rasha tayi watsi da ikirarin cewa ta kai harin Bam asibitin yara a garin Mariupol.
Rasha tace tsohon asibiti ne kuma tuni Sojoji sun kwace asibiti.
Mataimakin wakilin Rasha a majalisar dinkin duniya, Dmitry Polyanskiy,a shafinsa na tuwita yace:
"Haka ake fara yada labarun karya."
Polyanskiy yace tun ranar 7 ga Maris Rasha tayi gargadi an mayar da asibitin wajen fakewar mayaka.
Mutum 17 sun raunata a harin da aka kai asibitin yara dake Mariupol
Harin da kasar Rasha ta kai asibitin yara dak Mariupol ya bar mutum 17 a jikkace, cewar jami'an gwamnatin Ukraine.
Shugaban yankin Donetsk, Pavlo Kyrylenko, a bidiyon da ya daura shafin Facebook ya ce:
"Kawo yanzu mutum 17 sun jikkata a asibitin, babu yaron da ya jikta kuma babu wanda ya mutu."
Shugaban Ukraine ya yi Alla-wadai da harin da Rasha ta kai asibitin yara
Shugaban kasar Ukraine yace da gan-gan sojojin Rasha sun kai hari asibitin yara dake garin Mariupok inda akwai majinyata.
Yace:
"Mutane, yara yanzu haka na cikin rusassun ginin"
Biden ya godewa Koriya ta kudu bisa shiga jerin masu kin jinin Rasha
Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya aike wasikar godiya ga Shugaban kasar Koriya ta kudu, Moon Jae-in don shiga jerin kasashen da suka sanyawa Rasha takunkumi kudi da fitar da kaya.
Biden yace wannan babban goyon baya ne ga Ukraine, rahoton Aljazeera.
Mun kashe babban janar na Rasha, Ukraine
Hukumar Sojin Rasha ta bayyana cewa dakarunta sun hallaka Manjo Janar Vitaly Gerasimov kusa da garin Kharkiv.
Gerasimov ne babban kwamanda da biyu da Rasha zata rasa a yakin nan.
An kashe Gerasimov, wanda shine mataimakin kwamdanda rundunar 41 Army, ranar Litinin, ma'aikatar tsaron Ukraine ta bayyana.
Gwamnatin Ukraine ta bayyana cewa ta kashe Sojin Rasha 11,000 yayinda Rasha kuma ita tace 500 kadai aka kashe.
An fara kwasan fararen hula daga biranen Irpin da Sumy
Hukumomi a kasar Ukraine sun bayyana cewa an fara kwashe fararen hula daga birnin Irpin da Sumy bayan Rasha ta tsagaita wuta.
Ammam har yanzu ba'a san halin da fararen hulan Mariupol ke ciki ba saboda dakarun Rasha sun ragrgaza hanyoyin fita.
Fadar shugaban Rasha ta bayyana cewa ta tsagaita wuta don a kwashe faaren hula daga birnin Ukraine, Kyiv, Chenihiv da Kharkiv. Amma ba'a sani ko an fara kwashewan a halin yanzu ba.
Jami'an Sojin Rasha sun budewa motar yan jarida wuta
Dan jaridan kaar Siwzalan Guillaume Briquet ya tsallake rijiya da baya yayinda Sojojin Rasha suka budewa motarsa wuta a kudancin Ukrain ranar Lahadi duk da rubutun dake nuna cewa motar yan jarid ce.
Dan jaridan ya bayyana cewa kuna kokarin kasheshu ne kawai.
Kungiyar kare hakkin yan jarida ta bayyana cewa kaiwa yan jarida hari babban laifi ne.
A jawabin da ta saki a shainta na Tuwita, tace:
"Sakamakon hare-haren da dake kaiwa yan jarida masu daukan yakin dake gudana a Ukraine, muna kira ga yan jarida su bi a hankali."
Sama da mutum 1.7m sun gudu daga Ukraine: Majalisar dinkin duniya
Sama da mutane milyan daya da dubu dari bakwai sun gudu daga Ukraine, cewar majalisar dinkin duniya.
MDD tace fararen hula 1,735,068, mafi akasari mata da yara sun tsallaka bodar kasar kawo ranar Lahadi.
Za'ayi zaman sulhu karo na uku
Za'a shiga zaman tattaunawa na sulhu tsakanin wakilan Ukranie da Rasha misalin karfe 4 na rana agogon Kiev (2:00 Najeriya), daya daga cikin wakilai ya bayyana.
Rashata zata tsagaita wuta don kwashe fararen hula a birane 4
Dakarun Sojojin Rasha zasu tsagaita wuta don bada daman kwashe fararen hula a biranen ukraine hudu ranar Litinin.
Jaridar Interfax news ta ruwaito ma'aikatar tsaron Rasha ta fadi.
Ma'aikatar zata tsagaita wuta ne misalin karfe takwas na safe (agogon Afrika ta yamma) a biranen Kyiv, Kharkiv, Mariupol da Sumy.
Rasha ta lalata mana tashar jirgin saman Vinnytsia, Zelensky
Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana cewa an ragargaza tashar jirigin saman Vinnysia.
Volodymyr Zelenskyy yace:
"Yanzu aka sanar da ikan harin makami mai linzami da aka kai Vinnytsia, rokoki takwas... An lalata tashar jirgin saman gaba daya."
Kamfanonin katin ATM, Mastercard da Visa sun daina aiki a Rasha
Kamfanonin katin ATM, Mastercard da Visa sun sanar da dakatad da aiki a kasar Rasha cikin adawar da duniya ke yi da harin da ake kaiwa Ukraine.
Mastercard ya bayyana cewa duk katunanta da bankunan Rasha suka baiwa kwastamominsu a cikin kasar da wajen kasar, rahoton Aljazeera.
Kamfanin yace: “Da gaske muke”
A bangare guda, kamfanin Visa yana kokari tare da abokan harkarlarsu su dakatad da ayyuka a kwanaki masu zuwa.
Shugaban Visa Al Kelly yace:
“Dole tasa zamu dau mataki kan harin da Rasha ke kaiwa Ukraine.”
Putin: Ba zamu daina ragargazan Ukraine ba sai sun daina fada da mu
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyanawa Shugaban kasan Turkiyya, Tayyip Erdogan a wayar tarho cewa a zai daina kai hari Ukraine ba san burinsa ya cika kuma Ukraine ta daina fada da ita.
Fadar shugaban kasar Rasha, Kremlin, ta bayyana haka a wani jawabi, rahoton Aljazeera.
Rasha ta koma bude wuta a birnin Mariupol
Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa zata cigaba da bude wuta a birnin Mariupol awanni ayan sanar da tsagaita wuta.
A jawabin bidiyon da ma'aikatar ta saki, kakakin ma'aikatar Igor Konashenkov yace:
"Sakamakon rashin hadin kan Ukraine wajen tsawaita tsagaita wutan, mun cigaba da bude wuta a misalin karfe 18:00 agogon Moscow (4pm)."
An kashe farin hula sama da 350 a Ukraine, MDD
Akalla fararen hula 351 sun rasa ya tabbata sun rasa rayukansu a Ukraine, majalisar dinkin duniya ta bayyana.
Ofishin kwamishanan majalisar mai lura da lamuran kare hakkin bil adama ya bayyana cewa mafi akasarin fararen hulan sun mutu ne sakamakon bama-baman roka, makami mai linamu dss.
AlJaeera ya ruwaito ofishin da cewa:
“OHCHR ta yi imanin cewa adadin ya fi haka yawa, musamman a wuraren da gwamnatin kasar ke da iko har yanu a kwanakin nan."
Bayan tsagaita wuta, an dakatar da kwasan fararen hula daga Maripuol
Jami'an gwamnati a Mariupol sun bayyana cewa an jinkirta kwasan fararen hula daga garin saboda Sojin Rasha sun saba alkawarin tsagaita wuta.
Ita kuwa Rasha a martaninta tace sojojin Ukraine ne suka hana.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta tuhumi ya a mutun kasar Ukraine da hana fararen hula guduwa
Dakarun Sojin Rasha sun tsagaita a biranen Ukraine 2
Aljazeera ta ruwaito cewa dakarun Sojin Rasha sun tsagaita a biranen Ukraine biyu don a kwashe fararen hulan dake zaune a biranen.
Biranen sun hada da Mariupol da Volnovakha.
Jiya Wakilin Al Jazeera, Jonah Hull, ya ruwaito cewa Dakarun Sojin Rasha sun mamaye birnin Mariupol.
Bidiyon yadda aka yi raga-raga da birnin Borodyanka, kusa da Kyiv a Ukraine
Bidiyon da Aljazeera ta dauka ya nuna yadda artabu tsakanin Sojojin Rasha da Ukraine ya bar birnin Borodyanka, wanda ke kusa da babbar birnin kasa, Kiev.
Dakarun Rasha sun mamaye birnin Mariupol
Wakilin Al Jazeera, Jonah Hull, ya ruwaito cewa Dakarun Sojin Rasha sun mamaye birnin Mariupol.
Hull yace:
"Sun yanke wutan lantarki, sun datse layukan waya, sun hana kai kayayyaki"
"Saboda haka babu yadda za'a san takamammn abinda ke gudana ciki, sai dai wasu rahotanni dake cewa ana budewa garin wuta."
Dakarun Ukraine sun dakile Rasha daga shiga Mykolayiv, Hadimin Shugaban kasa Zelensky
Wani mai baiwa Shugaban kasa Ukraine shawara, Oleksiy Arestovych, ya bayyana cewa dakarun Sojin kasa sun dakile Sojin Rasha daga shiga garin Mylolayiv.
Ya bayyana hakan jawabi ga manema labarai na talabijin
Yace:
"Muna kyautata zaton dakile hare-haren da zasu iya kawowa - Zamu dakilesu a wasu wuraren ma."
Ba zamu shiga yakin Rasha da Ukraine ba, Shugaban kasar Belarus
Shugaban kasan Belarus, Alexander Lukashenko, ya bayyana cewa kasarsa ba zasu shiga yakin Rasha da Ukraine ba.
Alexander Lukashenko wanda abokin Vladimir Putin ne yace yayi hira mai tsawo da shi a waya ranar Juma'a.
Hukumar harkokin nukiliya na duniya IAEA tayi gargadi kan harin da Rasha ke kaiwa tashar Nukiliya
Hukumar IAEA ta yi kira ga Sojojin Rasha su daina kai hari tashar Nukiliyan Zaporizhzhia ksaboda akwai mumunan hadari idan aka fasa na'urorin nukiliya.
A jawabin da hukumar ta saki a shafinta na Tuwita, tace:
"Dirkta Janar na IAEA, @RafaelMGrossi, ya yi magana da Firai ministan Ukraine Denys Shmygal da hukumar lura da harkokin Nukiliyan Ukraine kan labarin wutan da ya tashi a Zaporizhzhia, ya yi kira ga a daina kai hare-hare saboda akwai hadari babba idan aka harbi na'urorin nukiliya."
Bayan ruwan wuta, Dakarun Rasha sun kwace tashar ajiyar Nukiliya na Zaporizhzhia
Dakarun Sojin kasar Rasha sun kwace tashar Nukiliyan Zaporizhzhia dake kudu maso gabashin Ukraine, a cewar jami'an gwamnatin Ukraine.
Wannan ya biyo bayan ruwan wutan da Rasha ta fara yiwa Zaporizhzhia da safiyar Juma'a.
Tashar ajiyar Nukiliya na Zaporizhzhia ya kama da wuta, cewar Magajin gari
Tashar ajiya Nukiliya dake Zaporizhzhia, kasar Ukraine ya kama da wuta, Magajin garin Enerdohar Orlov ya bayyana.
Wannan shine tashar ajiya mafi girma a fadin Turai
A cewarsa:
"Sakamakon harbe-harben da aka kaiwa gine-ginen tashar Nukiliya mafi girma a Turai, tashar Zaporizhzhia ya kama da wuta"
Jami'an kwana-kwana sun gaza kashe wutar da ta kama a tashar Nukiliyan Zaporizhzhia
Jami'an kwana-kwana sun gaza kashe wutar da ta kama tashar ajiyar Nukiliyan Zaporizhzhia sakamakon cigaba da kai hare-haren da Rasha ke yiwa tahsar, a cewar Nexta
Babban janar din sojin Rasha, Andrei Sukhovetsky, ya rasa ransa a Ukraine
Babban hafsin sojan kasar Rasha mai mukamin Janar, ya rasa rayuwarsa a yakin da suka kutsa kasar Ukraine.
Andrei Sukhovetsky, mataimakin kwamandan runduna ta 41 ya rasa ransa a jiya Laraba, jaridun kasar Ukraine suka ruwaito.
Kasar Rasha ta sanar da cewa: "Cike da matukar alhini muke samun mummunan labarin mutuwar abokinmu, Manjo Janar Andrei Aleksandrovich Sukhovetsky, a cikin Ukraine yayin da ya je aiki na musamman."
Rasha da Ukraine sun amince a baiwa yan bada agaji daman ayyukansu
Ukraine da Rasha sun amince a baiwa yan bada agaji daman kwashe masu farin hula a zaman sulhu karo na biyu da ya gudana yau, jami'in gwamnatin Ukraine ya bayyana.
A jawabin da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, mai baiwa shugaban kasa shawara Mykhailo Podolyak yace:
"An kammala zaman sulhu na biyu. Amma kash Ukraine bata samu abubuwan da take so ba tukun. An yanke shawara kan baiwa yan agaji dama ayyukansu."
Hakazalika wakilin Rasha a teburin sulhun, Vladimir Medinsky, ya tabbatar da sakamakon zaman sulhun yau da yiwuwar tsagaita wuta.
Kana tafka babban kuskure, Shugaban Faransa Macron ya gargadi Putin
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya gargadi Vladimir Putin da cewa yana tafka babban kuskure a Ukraine kuma abubuwan da gwamnatin ke yi zai illata Rasha nan da yan shekaru, kamfanin yada labaran Reuters ya ruwaito wani jami'in Faransa da cewa.
Wani hadimin Macron wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace Shugaban Faransan ya bayyanawa Putin haka ne lokacin da ya kirashi a waya.
A hirarsa da Reuters, hadimin Macron yace maigidansa ya fadawa Putin cewa:
"Karya kake wa kanka. Wannan zai illata kasarka kuma a karshe kowa zai rabu da kai, takunkumi zai raunataka."
An fara zaman sulhu karo a biyu
An fara zaman sulhu karo na biyu tsakanin wakilan Rasha da Ukraine.
Rahoton Aljazeera ya nuna cewa ana zaman ne a Brest, kudu maso yammacin Belarus.
Wakilin Ukraine, Davyd Arakhamia, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa kasarsa na shirin tattauna yada za'a baiwa yan bada agaji daman ayyukansau.
Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha
Najeriya na cikin jerin kasashen duniya 141 da suka kada kuri'a ranar Laraba a majalisar dinkin duniya don a hukunta Rasha bisa hare-haren da take kaiwa kasar Ukraine.
Hakazalika kasashen sun bukaci Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine kai tsaye.
Wannan zabe da aka kada ranar Laraba na nufin hukunta Rasha.
Cikin kasashe 193 da suka halarci zaman taron ganganmin majalisar tsaron, mutum 141 su zabi a hukunta Rasha.
Kasashe 35 sun janye daga zabe inda suka ce ba zasu ce hukunta Rasha ba kuma ba zasu ce kada a hukunta Rasha ba.
Kasashen sun hada da kasar Sin, Afrika ta Kudu, Mali, Madagascar, dss.
Kasashe 5 kuwa sun goyi bayan Rasha.
Sun hada da Syriya, Belarus, Koriya, Eriteriya da Rashan da kanta.
Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha
A karon farko, gwamnatin kasar Rasha ta bayyana adadin dakarun da ta rasa kawo yanzu tun lokacin da Vladimir Putin ya kai fara kai harin kwace Ukraine a makon da ya gabata.
Kakakin hedkwatan tsaron Rasha, Igor Konashenkov, a jawabin da ya saki a tashar Talabijin kasar ya bayyana cewa an hallaka Sojojinsu 498 a Ukraniya.
Yace:
"Sojojinmu dari hudu da casa'in da takwas sun mutu a faggen fama, kuma Sojinmu 1,597 sun jikkata."
Ranar farko: Yaki ya barke tsakanin Rasha da Ukraniya, Rasha ta fara kai harin bama-bamai
Dakarun Sojin kasar Rasha sun harba makami mai linzami cikin biranen Ukraniya yayinda Sojin kasa suke kokarin shiga, jami'an gwamnati da manema labarai sun bayyana.
Wannan ya biyo bayan sanarwar da Shugaban kasar Rasha, Vlamidir Putin, yayi cewa zasu fara kai hari gabashin Ukraniya.
Yan mintuna bayan sanarwar Putin a tashar Talabijin na kasar aka fara jin karar bama-bamai cikin birnin tarayyar Ukraniya, Kyiv.
Ministan harkokin wajen Ukraniya, Dmytro Kuleba, a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita yace:
"Putin ya fara kai hari Ukraniya. Ana kaiwa biranen Ukraniya hari."
Dakarun Sojojin Ukraine Sun Harbo Jiragen Yaƙin Rasha 5 Tare Da Helicofta
Dakarun Sojojin Kasar Ukraine sun harbo jiragen yaki biyar da kuma helicofta mallakar kasar Rasha, rahoton AFP.
Mai magana da yawun hukumar tsaro na Ukraine ya ce akwai yiwuwar daruruwan sojojin Rasha sun mutu sakamakon harin.
Hukumar tsaron iyakokin Uakraine ita ma ta ce harin sojojin na Rasha ya zo ne daga Belarus da ke makwabtaka da su.
Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya gargadi Amurka da sauran kasashen Turai su yi hattara kada su sa baki kan yakinsu da Ukraniya ko kuma su fuskanci mumunar ukuba, rahoton AFP.
Putin ya bayyana hakan ne da safiyar Alhamis yayinda yayi jawabi ga al'ummar kasar kan yanke shawarar kai hari Ukraniya.
Rasha ta kai hari tashar jirgin saman Ukraine, mutane da dama sun jikkata
Hotuna da bidiyo sun nuna yadda jiragen kasar Rasha suka kai hari jihohi a kasar Ukraine ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, 2022.
Rahoton Aljazeera ya nuna cewa kawo yanzu akalla mutum takwas sun hallaka yayinda Rasha ke ikirarin cewa ba tada niyyar kashe farin hula.
Rasha ta ragargaza jirgin da yafi kowanne girma a duniya dake kasar Ukraine
Kasar Rasha ta tarwatsa jirgin da yafi kowanne girma a duniya na kasar Ukraine - Antonov-225 jirgin saman Ukraine, wajen Kyiv a rana ta hudu da sojojin Moscow suka fara kai musu hari, kungiyar Ukrobironprom ta kasar Ukraine ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi.
Jirgin ya fita daban daga sauran jirage a fadin duniya, yana da tsawon mita 84 (sawun kafa 276) sannan yana iya daukar 250 tonnes(fan 551,000) na kaya, da gudun a kalla kilomita 850 a cikin awa daya 528 mph).
Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m
Biloniyan kasar Japan, Hiroshi Mickey Mikitani, a ranar Alhamis ya ce zai bai wa gwamnatin kasar Ukraine tallafin $8.7 miliyan inda ya danganta kutsen kasar Rasha da kalubale ga damokaradiyya.
Mamallakin e-commerce din a wasikar da ya aike wa shugaban kasar Ukraine, Volodymr Zelensky ya ce tallafin Yen biliyan dayan zai tafi ne wurin taimakon jama'ar Ukraine wadanda halin tashin hankalin nan ya ritsa dasu
Amurka, Birtaniya, kasashe 25 zasu taimakawa Ukraine da makamai
Kasashen duniya ashirin da bakwai (27) sun yi alkawarin aikewa jami'an Ukraine makamai, magunguna dss, Sky News ta ruwaito.
Wadannnan kasashe sun hada da Amurka, Birtaniya, da sauran kasashen nahiyar Turai.
Wannan ya biyo bayan ganawar bada tallafin kayan yaki da Sakataren tsaron Birtaniya, Ben Wallace, ya shirya da yammacin Juma'a inda kasashe 25 da suka hallara suka yi alkawari.
Kasashe biyun da basu samun daman halarta ba sun yi nasu alkawarin ranar Asabar.
Gabanin wannan sanarwa, Shugaban kasar Amurka ya rattafa hannu kan sabuwar umurnin baiwa kasar Ukraine tallafin kayan yakin $600m.
An kammala zama na farko don sulhunta tsakanin kasashen biyu
An kawo karshen tattaunawar zaman lafiya ta farko tsakanin tawagogin Ukraine da Rasha da aka yi a kan iyakar kasar da Belarus a yau Litinin.
Ba a bayyana sakamakon tattaunawar ba. Tattaunawar ta dauki sa'o'i da yawa kuma an raba shi gida biyu, in ji Jonah Hull na kafar labarai ta Al Jazeera, yana mai karawa da cewa tsayin taron ya nuna cewa akwai abubuwan da za a yi magana akansu.