Shugaban Koriya ta Arewa ya haramtawa 'yan ƙasarsa saka irin tufafinsa, ya hana shaguna sayar da irin tufafin
- Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-Un ba ya son mutane su kwafi irin salon sa sutturunsa kuma ga dukkan alamu da gaske yake
- Hakan yasa ya haramta wa kowa amfani da rigar sanyi irin ta fatar dabbobi don ya kasance shi kadai ne yake irin wankansa a gabadaya kasar
- Yanzu haka ya umarci ‘yan sandan kasar da su dinga yawata tituna su na kwace rigunan sanyi irin na sa daga jama’an da kuma shagunan sayar da sutturu
Koriya ta Arewa - Shugaban Koriya ta arewa, Kim Jong-Un ya haramta wa duk wasu ‘yan kasar kwaikwayon irin salon sutturar da ya ke saka wa.
Shugaban da gaske ya ke don ya umarci ‘yan sanda da yawata cikin kasar don kwace irin rigunan sanyinsa daga jama’a da masu shagunan da ke siyarwa.
Radio Free Asia sun ruwaito yadda aka haramta amfani da rigar sanyi ta fatar dabbobi don gudun kwafar salo irin na babban shugaban.
An ga ‘yar uwarsa, Kim Yo Jong sanye da irin kayan wanda su ka janyo shaharar sutturun a kasar cikin shekarar nan.
Yanzu haka samun sutturu irin na fatar dabbobi mai kyau a Koriya ta arewa gagarumin aiki ne don yanzu mutane su na ta nema a kasuwa. Sai dai kuma akwai ta boginta.
An dade ana amfani da rigunan sanyi na fatar dabbobi a Koriya ta arewa har sai da Kim Jong-Un ya yi kira da dakatar da amfani da su, kamar yadda Business Insider su ka ruwaito.
Kim Jon-Un ya yi hani da amfani da matsattsun jins inda ya ce shiga ce ta ‘yan jari hujja
Legit.ng ta ruwaito yadda shugaban Koriya ta arewa, Kim Jong-Un ya hana amfani da matsattsen jins a cikin kasar inda yace ‘yan jari hujja ne suke amfani da shi.
Ba wannan kadai ya hana ba, ya hana shiga iri-iri da gyaran gashi kala goma sha biyar. Sannan cikin salon da ya hana har da hujin hanci.
Kuma duk shigar da ya hana dole ne ta hanu a cikin kasarsa.
An yanke wa wani hukuncin kisa saboda fim ɗin 'Squid Game' a Korea ta Arewa
A wani labarin, kun ji cewa an yanke wa wani mutum dan kasar North Korea hukuncin kisa saboda yin smogal din fim din 'Squid Game' zuwa cikin kasar.
A cewar Radio Free Asia, an kama mutumin da ba a bayyana sunansa ba yana raba wa mutane fim din na kasar Korea ta Kudu.
An gano cewa ya shigo da fim din cikin kasar a boye ne cikin na'urar USB drive daga China.
Asali: Legit.ng