Abdullahi Abubakar
7276 articles published since 28 Afi 2023
7276 articles published since 28 Afi 2023
Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya yi magana kan shugabancin APC mai mulki inda ya ce kawai umarnin Bola Tinubu yake jira a kowane lokaci.
Rundunar yan sanda ta cafke wani magidanci dan shekara 70, Adamu Yakubu, kan zargin kashe 'yar uwarsa Hannatu Hashimu a Galadanchi a jihar Jigawa.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika, ya karyata rahotannin cewa ya fice daga jam’iyyar APC zuwa sabuwar kawancen adawa.
Wani matashin da ba a bayyana sunansa ba ya wallafa wani faifan bidiyo inda yake barazanar shiga cikin yan bindiga ko Boko Haram idan ba a taimake shi ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Bola Tinubu yayin da ya kai gaisuwar ta’aziyya ga dangin marigayi Aminu Dantata da ya rasu a makon jiya.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu masu makoki a kauyen Rim, jihar Plateau, inda suka harbi matashi.
Karancin albashi da ake biyan hadimin sanata a jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya, Tunbosun Awe ya ajiye aikinsa a matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasa.
Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya ce kawancen ADC ba shi da ƙarfi ko daidaito don fuskantar Bola Tinubu a 2027, ya ce PDP ce kaɗai ke da karfin takalar APC.
Yayin da aka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya, Gwamna Bassey Otu na Cross River ya sha alwashin cewa jihar za ta bai wa Tinubu kashi 96 cikin 100 na kuri’u.
Abdullahi Abubakar
Samu kari