Farashin kayayyakin masarufi a kasuwannin mu daga NAIJ.com
Wakillan mu daga Legit.ng a garuruwa daban-daban musamman ma a Arewacin Najeriya sun ziyarci kasuwannin garuruwan mu don binciko maku masu karatun kafar yada labaran mu yadda farashin kayayyakin masarufi suke.
Wakilan mu sun bayyana mana yadda sannu a hankali farashin shinkafar gida ke ta dada kara sauka.
Wannan a cewar yan kasuwar baya rasa nasaba da yadda manoma suka noma ita shinkafar sosai a daminar bana kuma anfanin gonar yayi albarka.
Haka zalika hakan ma ya yi matukar tasiri a kan yadda shinkafa yar-waje ita ma ta dan rage farashi a kasuwannin.
Har ilayau ma'aikatan namu sun fahimci cewar sauran kayayyakin abincin ma dai suna ta sauka sannu a hankali sakamakon kyaun da daminar bana ta yi.
Ku ci gaba da biyo mu don samun sahihan bayanai kan yadda farashin kayayyakin abinci suke a kasuwannin arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng