Wata mata ta banka ma wata mai ciki wuta

Wata mata ta banka ma wata mai ciki wuta

-Wata mata mai suna Lami tayi mummunan bakin ciki lokacin da saurayinta ya kyaleta ya auri wata               

- Taje gidansa ta banka ma matar sa Amina wuta

- Anyi saurin kai matar asibiti, a yanzu haka tana kan kulawa

An banka ma wata mata mai ciki wuta ba dadewa a garin Bauchi saboda takakkar da aka kawo mata kan mijin ta. Rohoton yace wanda  wata mata da ake kira Lami ta kaima wata mai ciki yar shekara 23 farmaki mai suna Amina Lawal a gidan mijinta.

Ance Lami ta watsa ma Amina fetur a jikin ta kuma sai ta banka mata wuta, Aminar dai ta samu kuna a matse-matsin ta da hannu da fuska.

Wata mata ta banka ma wata mai ciki wuta

Lami tace"Ina soyayya da mijin Amina kafin suyi aure kuma naji bakin cikin yin auren, tace" a hakikanin gaskiya banje da niyyar kona matar shi ba, niyya ta ita ce in kona duka gidan shi, ban ma san matar shi na cikin gidan ba, ya bata man lokaci da muna soyayya kuma sai ya kare da auren wata.

Wata mata ta banka ma wata mai ciki wuta

Amina tace wanda na mata maraba da ta shigo gidan, sai kawai naga ta fara watsa man fetur, kawai da tagama sai ta banka man wuta, na cire kayan jikina ina kokarin bude kofa, ashe kulle kofar ta bayan gidan, har sai da makobta sukaji ihu na ina cewa wuta!wuta! Sannan suka kawo man dauki.

Mijina ya fada man Lami tayi kokarin ganin ta hanashi aurena saboda tana son shi, amma be taba tunanin zata iya irin wannan aika-aikar ba.

Mijin nata Mustafa Ayodele yace wanda nayi sauri dan inje gida inga abunda ke faruwa, sai kawai na samu matata ta kone, mun kai kara gurin yan sanda wadanda ofishin su ke Yelwa, daga baya sai suka tura mu asibitin ATBU Bauchi.

Bantaba soyayya da Lami ba a rayuwa ta, ina kawai bata shawarari na yadda zata gudanar da rayuwar ta ne, dan me zata kaima matata farmaki kuma har da ciki take da shi na wata 3, saboda tana soba?

Wannan labarin ya nuna hatsabibanci irin na wasu mata, saboda sun kasa cigaba da rayuwar su kan tsoffin masoyan su, in kika mutum be aure ki ba, to be zabe ki bane a matsayin mata, ki cigaba da rayuwa kawai kin manta da cutar da akai ma ki, in kika bar ta a a rai, zaki iya aika ta wani abu makaman cin haka yabar ki da dana sani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng