Gwamna ya kafa tarihi

Gwamna ya kafa tarihi

- Gwamnan jihar Kogi ya kafa tarihi da nadin mace a matsayin babbar jami’ar mai hulda da ‘yan jaridu ta fadar gwamnatin jihar

- Yahaya Bello ya tabbatar da nadin Misisi Petra Akinti Oyegbule a kan wannan mukami a ranar Talata, 4 ga watan Oktoba

Gwamna ya kafa tarihi
Gwamna Yahaya Bello da sabuwar Kakakinsa Petra Akinti

Wacce gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya nada a matsayin babbar jami’arsa mai hulda da ‘yan jaridu, kuma mai magana da yawunsa ita ce Misisi Petra Akinti Oyegbule.

Kafin nadin nata dai, Petra ita ce hidimar gwamnan ta musamman a kan harkokin hanyoyin sadarwa na zamani.

A yanzu dai, ita ce farko da aka taba ba wannan mukami a Arewacin Najeriya, kuma ta biyu a duk fadin kasar.

Mai cike da murna da farin cikin da wannan nadi, Petra ta lika sakwannin godiya ga Allah da wannan dagawar likkafa, tare da godiya kuma ga ‘yan uwa da abokan arziki kan wannan sabon mukami a shafinta na sada zumunta da muhawara na Twitter.

A ‘yan kwanakin nan dai, likkafar mata na dagawa ta hanyar kafa tarihi dangane samun sabbi kuma manyan mukamai a fadin kasar a kuma fannoni daban-daban na rayuwa.

A jihar kano Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Aisha Muhammad Bello, mace ta farko a matsayin akanta Janar,  A Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo kuma, Amina Yahaya ce zama mace ta farko a tarihin siyasar dalibai a arewacin Najeriya ta zama shugaba a jami’ar,  sai kuma a ‘yan kwanakin nan a jihar Zamfara, a inda aka nada Hindatu Umar a matsayin shugabar karamar hukumar Argungu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel