Za a sake karrarama Fati Nijar

Za a sake karrarama Fati Nijar

- Za a karrama mashahuriyar mawakiya Fati Nijar a wani babban taro na mata da za a yi a Kano

- Mawakiyar ‘yar asalin Jamhuriyar Nijar ta shahara ne a wakokin zamani musamman a taron shagulgulan biki

- Kwanan baya ne masarautar Borgu ta karrama mawakiyar da sarautar gargajiya inda ‘yan uwa da abokan arzikin da kuma abokan sana’a suka halarta

Za a sake karrarama Fati Nijar
Fati Nijar da wasu abokan sana'arta na Kannywood

Likkafar Binta Labaran wacce aka fi sani da Fati Nijar ta yi gaba da wata karramawa da za a yiwa matashiyar mawakiyar a ranar Alhamis a 13 ga watan Oktoba na shekarar 2016 a garin Kano.

Kungiyar tallafawa mata a harkar kasuwanci da sana’a BWAEF ce ta shirya karrama Fati tare da wasu matan da suka yi fice a harkar kasuwanci da sana’a, suka kuma yi abin kuzo-ku-gani.

A cewar wani na hannun daman mawakiyar, Binta Labaran  ‘yar asalin jamhuriyar Nijar ce, ta yi fice a wakokin zamani a inda wakokinta suka yi farin jini da tsakanin matasa, Fati ta kuma yi suna wakokin da ta yi wa amare da ango a bukuwa a inda ta ke zuwa ta rera kai tsaye.

Za a sake karrarama Fati Nijar
Fati da wata babbar aminiyarta a lokacin bikin nadin Sarautar da aka bata a garin Borgu ta jihar Niger

Rahotanni na cewa, Fati ‘yar asalin jamhuriyar Nijar ta zo Kano ne a shekarun 1990  da ziyara, da kuma aniyar fitowa a fina-finan Hausa, ta samu kanta a waka ne a sakamakon hulda da Abubakar Sani mawakin finafinan da kuma sauransu da suke tashe a lokacin.

A kwanan baya ne masarautar Borgu a jihar Naija ta karrama Fati da sarautar gargajiya domin yabawa da irin gudunmawar da ta ke bayarwa wajen bunkasa harshen Hausa a wake-wakenta. An kuma gudanar da kasaitaccen bikin nadin sarautar a garin, inda ‘yan uwa da abokan arziki da kuma abokan sana’arta suka halarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel