Masana sun nemo maganin cutar Kanjamau watau AIDS
– Malaman Kimiyya sun gano maganin cutar nan mai karya garkuwar jikin dan Adam
– Wasu masu bincike a Kasar Birtaniyya sun nemo maganin cutar kanjamau da aka fi sani da AIDS da Turanci
– Yanzu haka har an yi maganin cutar ta SIDA ko AIDS a jikin wani Bature
Da alamu dai Turawa na daf da gano maganin cutar nan mai karya garkuwar jikin bil adama wanda aka sani da Kanjamau, a Turance kuma ana kiran ta HIV AIDS. Huffington Post ta rahoto cewa yanzu haka har an yi wa wani ma’aikaci a Kasar Birtaniya magananin wannan cuta, kuma har ya warke.
Bayan an yi wasu magunguna sai ga shi an samu wannan maras lafiya ya murmure, cutar ta fice daga jikin sa. An dai yi wa wannan mutumi wata allura ne, wanda ta gano kwayoyin cutar, daga nan kuma aka yi amfani da wani magani mai suna Vorinosat, hakan ya taimaka wajen kashe cutar daga jikin sa.
KU KARANTA: Aljanu sun kama wani dan majalisa
Shi wannan magani na Vorinosat, ana amfani da shi wajen maganin cutar Cancer, yana kokari wajen kashe duk wasu kwayar rai da suka kamu da cuta. Masana dai sun ce wannan maganin ya dauko hanya wajen kawo karshen wannan masifaffen cuta a duniya. Haka kuma yanzu ana kokarin gwado karfin sa ne.
Yanzu haka dai ana bukatar auna karfin wannan magani a jikin mutane 50, wanda zai bada damar gane karfin maganin idan har dukkanin su kowa ya warke.Cutar HIV idan ta zama AIDS dai tana karya garkuwar jikin dan adam. Kawo yanzu dai ba ta da wani magani a duniya.
Asali: Legit.ng