Ya samu karuwa Yan-Uku sati daya bayan korarsa daga aiki
Kamar yadda hausawa ke cewa, wani hani daga Allah baiwa ne, sai dai dayawa daga cikin mutane basa gamsuwa da haka, domin wani mutum Allah ya bashi kyautar karuwar Yan-uku.
Wani tsohon ma’aikacin Banki dan shekaru 40 mai suna Luke Anyaechie ya rasa aikinsa da sati daya kenan, sai Allah ya bashi karuwa na ban mamaki, yayin da Allah ya ba matarsa haihuwa yaya yan-uku, inji jaridar Punch.
KARANTA:Yar shekaru 30 ta auri mai shekaru 100
Sai dai ana tunanin yadda Anyaechi zai kula da matarsa tare da yaya ukun tunda dai a yanzu ba shi da aikin yi, amma Anyaechi yace: “Ina da tabbacin Ubangiji daya bani wadannan yaya, zai kawo yadda za’ayi, duk da halin tattalin arziki da kasar take ciki.
“Kuma a matsayi na Kirista, na mika komai ga Ubangiji, kuma ba zai bani kunya ba.”
Daga nan yace samun yan-uku ba karamin abin al’ajabi bane.
Asali: Legit.ng