Zuckerberg ya kara harshen Fulatanci a Facebook

Zuckerberg ya kara harshen Fulatanci a Facebook

Shafin sada zumunta na Facebook ya kara harsuna uku, da suka hada da Fulatanci a cikin harsunan da mutane za su iya amfani da shafin, yarikan da aka sanya sun hada da  Fula wato Fulatanci, Maltese da Corsican.

Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg wanda ya sanar da hakan ya ce yanzu akwai harsuna sama da dari kenan da ake amfani da su a shafinsa.

Mista Zuckerberg ya ce akwai fiye da mutane biliyan daya a duniya dake amfani da wani harshe daga a shafin na Facebook daga cikin harsunan wanda kuma ba Turanci ba.

Zuckerberg ya kara harshen Fulatanci a Facebook
Shugaban shafin Facebook Mark Zuckerberg

"A yanzu shafin Facebook na da harsuna sama da dari- tare da mutane sama da miliyan daya dake amfani da wani harshe ba na Turanci ba, a yau mun kara Fula, Maltese da kuma Corsican"

"Hakan ya faru ne da taimakon al'umman mu,a shekaru da suka wuce, daruruwan dubban mutane sun hadu tare don samar da fassarar kalmomi da ya dace a Facebook saboda ma'anar abu a Turance zai iya zama wani abu daban a Larabci ko yaren Japanese."  cewar Mark Zukerberg.

Ya ce a cikin shekaru goma da suka wuce, dubban mutane sun taimaka wajen fito da fassarar kalmomi da jumloli da za a iya amfani da su a Facebook.

Harshen Fula wanda aka fi sani da Fulatanci da aka kara a shafin na Facebook, ana amfani da shi sosai a Najeriya, musanman a arewa maso gabashin kasar, da ma wasu kasashe kimanin ashirin a yammaci da tsakiyar Afirka. A wasu kasashen kuma suna amfani da shi a matsayin yare na biyu kamar irinsu al’umman Kirdi na arewacin kasar Kamaru.

A baya shafin na Facebook ya sanya harshen Hausa, sannan ya sha alwashin kara wasu harsunan domin ba jama'a damar yin mu'amala da wadanda suke so cikin sauki.

Ku tuna a ranar 30 ga watan Augusta Mark Zuckerberg ya ziyarci kasar Najeriya inda ya hadu da masana’antun na’ura mai kwakwalwa a jihar Lagas ya kuma yi alkawarin kara harsunan kasar Najeriya a shafin na zumuntar Facebook.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng