Najeriya zuwa Kasar Afrika ta kudu a Jirgi N35000

Najeriya zuwa Kasar Afrika ta kudu a Jirgi N35000

Kudin Jirgin sama ya sauko kasa saboda Bikin ‘yancin Kai a Kasar Najeriya

Sai kaje Afrika ta kudu ka dawo duk a Dala 256 a Kamfanin Jirgi na South African Air

A yau ne dai Najeriya ta ke cika Shekaru 56 da samun ‘Yancin kai daga turawan mallaka

Najeriya zuwa Kasar Afrika ta kudu a Jirgi N35000

A yayin da ake bikin murnar samun samun ‘Yancin kai na 56 a Najeriya, Kasar Afrika ta Kudu ta taya Najeriyar murna ta hanyar rage farashin kudin Jirgi zuwa Kasar. Yanzu da dala 256 kacal, sai mutum ya hau jirgi har Birnin Johannesburg na Kasar.

Jirgin South African Airways na bada kujerar garabasa zuwa Kasar, daga Najeriya; ta Legas ko Abuja, mutum zai isa Babban Birnin Kasar Afrika ta kudu a jirgi ba tare da ya kashe fiye da kudi Naira 35000 ba. Da dala kusan 250 mutum zai hau jirgi tun daga Kasar nan har Kasar Afrika ta kudu, kuma har ma ya ci kwai da biredi a hanya.

KU KARANTA: An dakatar da wasu manyan makaranta a Najeriya

Babban Kamfanin Jirgi na South African Air na taya Kasar Najeriya bikin ‘Yancin kai na 56 ne ta hanyar bada garabasar tikitin Jirgi zuwa Kasar a kan Dala shi ma 256. Wannan kuwa ba karamin sauki bane idan aka duba. Kamfanin Jirgi nan dai zai cigaba da taya Najeriya bikin samun ‘Yancin kan har zuwa karshen watan gobe. Domin samun wannan dama sai mutum ya garzaya adireshin wannan jirgi a; www.flysaa.com.

A yau ne dai Najeriya ta cika Shekaru 56 daidai da samun ‘Yancin kai daga turawan mallaka na Kasar Ingila. Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari yayi jawabi ga daukacin al’ummar Kasar game da inda aka dosa da kuma yadda abubuwa suke a Kasa. Haka nan kuma Tsohon Shugaba, Dr. Jonathan Goodluck ya aika da na sa sakon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng