Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

– Shugaba Muhammadu Buhari ya mulki Kasar nan a lokacin Soji daga Disamban 1983 zuwa Agustan shekarar 1985, a ranar 29 ga watan Mayun bara kuwa ya kara darewa mulkin Kasar, a matsayin Shugaban farar hula

– Sanannen abu ne cewa Shugaba Buhari ya dade yana neman takarar Shugabancin Kasar nan, har yayi ya gaji. Har sai shekarar 2015, inda ya samu sa’ar buge tsohon shugaba Jonathan Goodluck

– Mutane da dama dai ba su yi amanna da Buhari ba saboda suna ganin cewa, ba zai taba barin halin sa na Soja ba. Duk da cewa ya sha jaddada riddar sa gaban duniya

Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

 

 

 

 

 

Duk da cewa wani zai iya ce maka ai tuwo ba ya taba canza suna. Ko a yanzu a mulkin Shugaba Buhari an zarge sa da karya hakkin bil adama, kamar yadda ya kama Sambo Dasuki, Nnamdi Kanu da Ibrahim Zakzaky ya garkame. Ga shi ya rufe hanyoyin shiga na ‘border’ kamar yadda dai yayi a baya, ga wani tsarin kasuwanci da yake kokarin kullawa da Kasar China, dsr dai. Ga kuma yunwar Buhariyyah, ta dawo…Sai dai mun kawo maku irin bambancin da aka samu tsakanin zuwan Shugaba Buharin na farko da kuma na yanzu:

Babu irin matsin da Shugaba Buhari bai sha ba a shekarun 84-85 na ya cire tallafin man fetur, da na sauran kayayyaki; Sai dai Janar din ya hau kujerar na-ki, yace sam ba zai yi hakan ba, don talakawa. Sai ga shi abin mamaki, wannan karon ya cire tallafin man fetur din. Ko a zamanin Shugaba Jonathan, Buhari bai amince da cire tallafin ba. Wannan karan kuwa, dara ta ci gida, sai dai ‘Yan Najeriya ba su yi masa bore ba. A baya dai Najeriya ta saba biyan kudi da ya kan wuce Naira Tiriliyan guda kan tallafi, mafi yawa kuma ana tunanin aljihun bogi yake zarcewa. Yanzu dai man fetur din da Najeriya ta ke sha ya ragu, da alamar tambaya.

Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

Haka dai a wancan lokaci, cikin sharuddan da Kungiyar IMF ta ba sa, akwai karya farashin kudin Naira, nan ma Janar Buhari yace ‘Ina’ Kamar dai batun ‘Subsidy’, Bankin CBN na Kasar ya saki farashin kudin Nairar a sama yana lilo-inda kasuwa ta kada da shi, ba dai kamar yadda Shugaba Buhari ya so ba. Farkon hawan mulkin sa, yayi kokarin tokare darajar Nairar da ‘Yan dalar da Kasar ta ke da su, sai dai aikin ya wuce nan.

Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

Aiki da Majalisa bakon abu ne wajen Shugaba Janar Buhari, ya kuwa yi iya bakin gwargwado. Tun fari, Shugaba Buhari yace ba zai tsoma baki cikin sha’anin zaben Majalisun Kasar ba, yin hakan dai ya zo da irin na sa cikas din. Ba kamar yadda yayi a baya ba, sai dai kawai Fadar Koli ko na Tarayya na Soji ‘Supreme Military Council’ da ‘Federal Military Council’ ta murza gashin baki, tace ga yadda za ayi. Asali ma dai Shugaban na da kudurori da dama gaban Majalisar, tun bara wanda sun ki cewa ko ‘hmm’, wasu kuma na tafe, ko ya za a kaya? Ko dai fita Kasar waje Shugaban Kasar zai yi, sai ya rubutawa Majalisar takarda. Ga batun kasafin kudi da aka yi ta fadi-tashi.

Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

 

 

 

 

 

 

 

 

Buhari a gaban Majalisa

KU KARANTA: Ko dai mulkin Kasar nan gadon gidan Arewa ne?

A shekarar 1984, Shugaba Buhari ya kirkiro wata Doka mai lamba 4, wanda tace duk dan jaridar da ya rubuta karya game da Gwamnati, zai sha dauri ko tara na kudi. Hakan ta sa aka daure wasu ‘yan jarida a Kasar, a bara wani Sanatan majalisar Dattawa na Kasar nan, ya nemi ya kawo irin wannan kudiri a Majalisa, sai dai tuni Shugaba Buhari yace wannan ba da shi ba.

Dole wannan karo Shugaba Buhari ya bi kundin tsarin mulkin Kasa wajen nada Ministoci, bayan dogon lokaci, ya nada Ministoci; guda daya daga kowace Jiha. Ba kuwa haka aka saba a mulkin Soji ba, ka iya ganin wata Jiha ba ta da wakili a Majalisar zartarwar. Sai dai Buhari ya nada kan sa a matsayin Ministan man fetur, ko can dai ya rike irin wannan matsayi a baya kafin ya zama Shugaban Kasa.

A wancan karo ba a san Matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba sosai-Hajiya Safinatu. A bara kuwa wajen yakin neman zabe, ‘Yan Najeriya sun ga Aisha Buhari-Matar Muhammadu Buhari. Ta kuwa yi alkawari kamar na mai gidan ta, cewa ba za ta kama Ofis ba na ‘Uwargidan Najeriya’ kamar yadda aka saba don ya saba dokar Kasa. Sai ga shi yanzu ta kan je har Amurka, har da mai mata kwaliyya, amma a matsayin ‘Wife of the President’ ba kuwa ‘First lady’ ba, watau Matar Shugaban Kasa, ba Uwargidan sa ba. To ai an ki cin biri, an ci dila.

Shugaba Buhari; Jiya ba yau ba

 

 

 

 

 

 

Aisha Buhari da matar Shugaban Kasar Amurka

Bayan hanbarar da Gwamnatin Shehu Shagari, Buhari ya rage kasafin kudin Kasar na shekarar da ta biyo, sai dai wannan karo, Shugaba Buhari ya ma kara karfin kasafin Kudin Kasar Najeriya ne a wannan shekarar, daga Tiriliyan hudu da rabi zuwa fiye da Tiriliyan shida.

Kamar dai yadda ya kara karfin kasafin kudin Kasar nan, Shugaba Buhari ya kara yawan kudin da aka ware na ayyuka-irin su tituna, gada, gidaje dsr. Shugaban Kasar ya ware kusan rabin Tiriliyan wajen wannan, ba ma za a hada da abin da Gwamnatocin baya suka saba ba. A shekarun Soji kuwa, Buhari YA tsaida duk wasu manyan ayyuka da Shagari ya fara, da cewar babu kudi. Haka kuma akwai shirin daukar ma’aikata da dama har sama da 500000, a mulkin Soji kuwa, Janar Buhari yayi sanadiyyar rasa aikin mutane dubunnai.

A lokacin Soji, Janar Buhari ya harbe wadanda aka kama da laifin safarar kwayoyi har lahira, mace da namiji, babba da yaro. A wani kaulin, wannan na daga cikn dalilin da ya sa aka kifar da Gwamnatin sa. Sai dai wannan karo babu wata doka mai kama da wancan mai lamba ta 20. Amma dai, ‘Yan Kwastam da Ma’aikatan hanyoyin ruwa sun rufe shigo da kayan jabu.

A lokacin mulkin Soji, Buhari ya haramtawa masu rike da Jihohin Kasar cin bashi ko ta wani iri. Kamar dai yadda ya karbi (ko ace ya kwata) mulkin Kasar daga hannun Shagari, Gwamnoni da dama sun gaza biyan albashin Ma’ikatan su, a mulkin Tsohon Shugaba Jonathan. Gwamnatin Buhari ta bada aron kudi domin a biya ma’aikatan Jihohi, kwanan nan ma kum, Gwamantin Tarayya ta kara fito da wani sabon tsarin rancen ga Gwamnatin Jihohin Kasar.

Har yanzu dai babban dodon da Shugaba Buhari yake fada da shi, shi ne Rashawa a Najeriya. Ko da dai bai sauka daga wannan matsayin ba, sai dai salon ya canza. A zamanin Soji, ya kama ‘yan siyasa da dama ya daure, sai dai kowa tashi ta fishe shi. Yanzu kuwa, tsarin mulkin Kasa yace 'barawon da ba a kama ba, sunan sa Muhammadu', ba kamar da can da Buhari ya rika amfani da tsarin ‘Na shiga ban dauka ba... ba ta fitar da barawo’ ba. Da bakin sa yace yanzu sai ya ga wadanda suka shiga Gwamnati a cikin manyan motoci, amma tsarin mulki yace har sai an kama su da laifi baro-baro sannan suka zama barayi. Ba don haka ba da tuni an maimaita na Ummaru Dikko da Deziani Madukwe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng