Wakilin jam’iyyar APC ya yanke ya mutu a Edo

Wakilin jam’iyyar APC ya yanke ya mutu a Edo

Zaben Edo ya wuce ya bar baya da kura, saboda an samu farfagaba a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba yayin da ake gudanar da zaben gwamnan jihar Edo.

Wakilin jam’iyyar APC ya yanke ya mutu a Edo

Fargaban ya faru ne sakamakon rasuwar wani jami’in APC a rumfar zabe na kasuwar Abico a mazaba na 10 da 8 dake karamar hukumar Ikpoba-Okha na jihar inda wakilin jam’iyyar APC a rumfar zaben ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani wakilin APC mai shekaru 58 mai suna Solomon Omorogbe ya isa rumfar da zai kada kuri’an sa da sanyin safiyan laraba, tare da tsare kuri’un jam’iyyar APC. Rahoton ya cigaba da cewa jim kadan bayan kada kuri’an nasa kenan, Solomon ya yanke jiki, ya mutu.

KU KARANTA: Sojan Najeriya ya taimaka wajen karbar haihuwar wata mata

Nan da nan babban dan san Charlie tare da sauran jama’a suka garzaya da mamacin zuwa asibitin Akugbe, bayan isan su Asibitin ne likitoci suka tabbatar da rasuwar mutumin.

An gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar laraba 28 ga watan satumba, inda al’ummar garin sukayi fitar farin dango suka kada kuri’un su, sai dai bayan kammala tattara kuri’un ne hukumar zabe (INEC) ta tabbatar da Godwin Obaseki na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 319,483.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel