Wani dalibi dan baiwa a Jami’ar ABU Zaria yayi bajinta

Wani dalibi dan baiwa a Jami’ar ABU Zaria yayi bajinta

- Wani Dalibi a Jami’ar Ahmadu Bello, ABU Zaria mai suna Shettima Kyari Ali ya kera wani dan karamin jirgi

- Hazikin dalibin yayi wannan aiki ne a matsayin aikin kundin digirin sa na farko

- Shettima Kyari ya sadaukar da aikin sa ga ‘Yan matan Chibok da ‘Yan Boko Haram suka sace

Wani dalibi dan baiwa a Jami’ar ABU Zaria yayi bajinta

 

 

 

Wani dalibi dan baiwa a Jami’ar Ahmadu Bello, ABU Zaria mai suna Shettima Kyari Ali ya kera wani dan karamin jirgin yawo da ake kira ‘drone.’

Shettima dalibi ne a Jami’ar Tarayyar da ke Zaria, yana karantar Ilmin kimiyyar ‘Physics’, wanda yanzu haka yake rubuta kundin kammala digirin nasa.

Malam Shettima yayi wannan aiki ne a matsayin kundin digirin sa, ya kuma sadaukar da aikin ga ‘yan matan Chibok din nan da ‘yan Boko Haram suka sace fiye da shekaru biyu da suka wuce. Shettima Ali dai ya kira wannan gagarumin aiki da suna ‘Hope for Chibok Girls’, watau dai akwai rabon ganin badi ga matan da aka sace.

KU KARANTA: Wani matashi dan Kaduna ya kirkiro manhaja da za ta ceci rai

Shettima dai babarbare ne, amma yana zaune, da kuma karatun sa a Garin Zaria. Shettima yayi Makarantar Nuhu Bammalli da kuma Firamaren Makarantar Koyon tukin Jirgi a Garin. Yanzu haka, Shettima na shirin kammala karatun digirin sa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Wannan jirgi dai shi kadai yake tashi, ya kuma sauka abin sa. Haka kuma akwai damar daukar hoto da magana, kai jirgin na iya fahimtar cewa akwai hayaki a kusa. Kwanakin baya dai mun kawo muku labarin wani tsohon dalibin Jami’ar ta Jami’ar Ahmadu Bello da ya kirkiro wata manhajar kare hadura a Kasar. Wannan abu ne mai kyau kwarai da gaske, musamman ganin matasan mu ne. Dama dai wai taken makarantar, ko daga ina kake, dalibin ta yayi maka nisa.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel