Tofa: Kudin makaranta sun bace a FCE Zaria
– Rahotanni daga Jaridun Kasar nan sun bayyana cewa an karkatar da kudi N26m daga asusun Kwalejin Ilmi ta Zaria watau FCE Zaria da ke Jihar Kaduna
– Wannan dai kudin makarantar daliban makarantar ne, sai dai ba a san inda suka shiga
– Jami’an ‘yan Sanda da kuma Hukumar Makarantar sun fara binciken yadda aka yi kudin suka salwanta
Tirkashi. An samu labarin wata badakala da ta shiga Kwalejin Ilmi ta Zaria watau FCE Zaria. Bayan da dalibai suka biya kudin makaranta, an samu labarin cewa gaba daya kudin sun bi iska. Jaridar Premium Times ta rahoto labarin daga Hukumar dillacin labarai, NAN ta Kasa cewa kudin makarantar daliban FCE Zaria sun bace daga asusun Makarantar.
Hukumar dillacin labarai, NAN ta bayyana cewa Naira Miliyan 26 sun yi kafa daga asusun Makarantar. Kudin makarantar dalibai har 1, 128 sun shiga rububi a yanzu haka, bayan da Bankunan Garin ba su saka kudin cikin asusun Makarantar ba. Hakan dai ya sa hanakalin daliban ya tashi. Wasu daga cikin dalibin makarantar sun bayyana cewa dai wannan cuwa-cuwar daga Makarantar ne da kuma Bankunan Garin. Wani dalibi a Makarantar ya tabbatar da cewa ya biya kudin makarantar a Bankin Sabon Gari da hannun sa, yace sai kuma yaji labarin kudin ba su shiga asusun bankin makarantar ba.
KU KARANTA: Nasarorin da Najeriya ta samu-Shugaba Buhari
Wani dalibin yace shi ma ya biya kudin makarantar, sai dai har yanzu ba ayi masa rajista ba, kuma ire-iren su da suka samu wannan matsalar suna da dama. Yanzu haka dai fiye da dalibai 1,000 suna fama da wannan matsalar. Akwai wanda ya bayyana cewa yana tare da takardun shaidar biyan kudi a banki, sai dai har yanzu an ce bai biya kudin makarantar ba.
Ma’ajin makarantar, Mohammed Sani-Uwais yace za su sa ayi bincike game da batun; yanzu haka ‘Yan sanda suna bincike, kuma Hukumar Makarantar ta kafa kwamitin bincike.
Asali: Legit.ng