Mai tallan kayan itace yaci zanzaro
- An gano wani mai tallan kayan itace da zanzaro a kasar Ghana
- Kaman yadda Abdullahi yayi a Najeriya, shin wannan wata sabon salon kasuwanci ne?
Domin cigaba a kasuwanci a yau, dole ne mutum ya samar da sabbin salon yin kasuwanci. Wani mai talla a Ghana ya dau wannan shawaran ga kan sa.
Duk wanda ya gan shi zai dauka wani ne ya sauka daga motarsa ba tare da sanin talla ya keyi ba. Wannan bawan Allah sanya kayan itacen cikin roba sanye da sunansa.
KU KARANTA: Wannan kerkecin yanayin abubuwa irin na mutane
Irin wannan dabi’an kadai zai sa mutane suyi masa ciniki. Kuma ya sanya kaya mai launin tutan kasar Ghana,wanda yake nuna cewa yana kishin kasan sa duk da cewa gwamnati bata bashi aikin yi ba.
A yanzu, jama'ar Najeriya suke yi iri irin ayyukan da samu kudi, domin suke cewa wanda tattalinn arzikin kasar Najeriya ta koma.
Asali: Legit.ng