Premier League: Arsenal ta casa Chelsea
– Dan wasa Theo Walcott, da Alexis Sanchez su zura kwallaye a karawar su da Chelsea a wasan Premier League na Ingila
– Arsenal ta dirkawa Chelsea kwallaye uku da nema a filin wasa na Emirates da ke London
– An fi shekara uku Arsenal ba ta ci Chelsea ba a Premier League
Kungiyar Arsenal ta koyawa Chelsea hankali a wasan su da suka buga Ranar Asabar a Filin Emirates na Arsenal. Arsenal dai ta bude cin nata ne ta kafar dan wasa Alexis Sanchez; wanda ya dasawa Gola Thibaut Courtious kwallo a ragar sa, bayan karbe kwallo daga hannun dan bayan Chelsea Gary Cahill tun a tsakiyar fili.
Bayan minti biyu sai ga dan wasa Theo Walcott ya kara ta biyu, Alex Iwobi da Mesut Oezil da kuma Alexis Sanchez ne suka yi wani wasa kafin a kawowa Walcott kwallon. Ana daf da zuwa hutun rabin lokaci a wasan ne Arsenal ta kara kwallo na uku, Oezil Mesut ya yanke N’Golo Kante, hakan yayi sanadiyar cin kwallon.
KU KARANTA: Conte ya hana yan wasan Chelsea cin gurasa
Wannan ne dai karo na farko da Arsenal ta doke Chelsea cikin shekaru kusan biyar, wannan gagarumar nasara ta sa Arsenal ta dawo ta uku a teburin gasar Premier league, yayin da Man City ta ke sama, sannan kuma Kungiyar Tottenham, na biyu. Kungiyar Chelsea dai ta Antonio Conte ta jera wasanni uku kenan, ba tare da cin ko daya baa Gasar Premier League. Kafin nan kuwa Arsenal ta doke Nottingham Forest da ci har 5-0, inda ita kuma Chelsea ta doke Leicester City daga baya, duk a Gasar cin Kofin Ingila.
Dan wasa kuma Kyaftin din Arsenal, Per Mertesacker bai samu buga wasan ba saboda lalurar rashin lafiya. Haka kuma dai Danny Welbeck, da dan wasan tsakiyar nan Aaron Ramsey. Chelsea ma ta take wasan ne ba tare da Kyaftin din ta ba, John Terry. Rabon Chelsea dai da rasa wasa a gidan nan, tun shekaru shida da suka wuce.
Asali: Legit.ng