Man Utd ta dagargaza Leicester City a Firmiya

Man Utd ta dagargaza Leicester City a Firmiya

Pogba ya ci kwallon farko a Man Utd

– Sabon dan wasa, kuma wanda yafi kowa tsada a duniya, Paul Pogba ya ci kwallon sa na farko a Man Utd

– ‘Yan wasa Chris Smalling, Juan Mata da Rashford sun jefa kwallaye a karawar Man Utd da Leicester City

– Kocin Man Utd din Jose Mourinho ya dai samu sa’ida, bayan ya rasa wasanni biyu a jere a Gasar EPL din

Man Utd ta dagargaza Leicester City a Firmiya

 

 

 

 

Kungiyar Man Utd tayi kaca-kaca da Zakarun Gasar Premier league ‘Leicester City a filin Old Trafford a Jiya Asabar. Cikin kankanin lokaci Man Utd ta zura kwallaye hudu a wasan, Dan bayan nan watau Chris Smalling ya fara leka ragar, kana said an wasa Juan Mata. Marcus Rashford ya ci kwallo na uku, sai kuma dan wasan da yafi kowa tsada a duniya, Paul Pogba ya ci kwallon karshe, kuma ta sa ta farko a Man Utd.

KU KARANTA: Labarin dan wasa Paul Pogba

Jose Mourinho ya fara da Rooney bisa teburin benci, hakan kuma ya taimakawa Man utd din wajen sauri da kwallo. Bayan an zubawa Kungiyar Leicester kwallaye da dama sai Kocin Kungiyar, Claudio Ranieri ya canza Jamie Vady da Riyad Mahrez a hutun rabin lokaci, ya kuma sako Andy King da Demerai Gray. Gray din ne kuma ya ci wa Leicester kwallo dayar da ta samu.

An dai samu dan wasa mai tsada a duniya, Paul Pogba yaci kwallon sa na farko a Kungiyar ta Man Utd, Pogba ya ci kwallon ne da kai. Bayan ya jefa kwallon a raga da kai da karfin tsiya, ya ruga a guje yaje yayi rawan ‘dab’ don murna.

Leicester dai ta kara shan kashi hannun Jose Mourinho wani karo, a farkon Gasar bana, Man Utd ta buge Kungiyar Leicester City a wasan cin Kofin Community Shield, da ci biyu da daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng