Hoton yan hudun gwamnan jihar Bayelsa
Hotunan farko na yan hudun da gwamnan jihar Bayelsa, gwamna Henry Seriake Dickson ya Haifa ya faso.
Dickson da matar sa sun yi aure tsawon shekaru da dama ba tare da sun samu haihuwa ba. Ma’auratan a yanzu sun samu albarkan yara hudu a lokaci daya, namiji daya da mata uku.
Yan hudun gwamnan jihar Bayelsa
KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya na harin gwamnatin Buhari kan bashi
Babban sakataren labarai na Gwamnan, Daniel Iworiso-Markson, ne ya sanar da haihuwar farincikin, ya bayyana cewa ma’auratan sun kasance cikin farin ciki a yayinda suka tarbi yaransu mata uku da kuma namiji daya a ranar Juma’a 23 ga watan Satumba, na shekara 2016 a kasar Amurka.
Haihuwar yaran ya zama murna biyu ga gwamnan kamar yadda yake cikin farinciki a zaben da aka basa a wani babban kotun Abuja a ranar Alhamis 22 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng