An kama wani dan shekara 20 ya ma yar shekara hudu fyade

An kama wani dan shekara 20 ya ma yar shekara hudu fyade

Wanda ake zargi da fyaden da aka bayyan a matsayin Bassey Johnson, Wanda yake da shagon, ance ana zarginsa da yima wata karamar yarinya fyade lokacin da suka shiga dakinsa ita da yayan ta Wareed dan suyi kallo a gidan Johnson.

Johnson dan shekara 20 wanda makoci ne ga iyalan yarinya da aka bayyan sunan ta Fatima a unguwar Idimu Lagos, ya bar yaran su shigo dakinsa misalin karfe 9 na safe ranar lahadi, shine yayi amfani da damar yayi ma Fatima fyade, a lokacin kuma bacci ya dauki yayan ta.

Kamar yadda makocin su ya bayyana mai suna Adeyinka yace, an gano amma yarinyar fyade bayan mamar Fatima ta lura da yarinya ta kasa dena taba al'aurar ta.

Bassey Johnson makoci ne na kusa ga iyayen yarinyar, makota ne, sa'annan yaran sun saba zuwa suyi kallo a dakin, ranar wannan lahadin yarinyar da yayan ta sun shiga daki Bassey suna kallo sai yayan ta yayi bacci, shi kuma yayi amfani da damar yama yar karamar yarinyar fyade.

Kara karanta wannan

Hotuna: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya lale N10m, ya siya fom din takarar majalisar wakilai

Bayan yarinyar ta fito daga dakin, sai mamar ta ta lura da yarinyar ta ki dena kuka, kuma ta kas dena taba al'aurar ta, lokacin da mamar ta duba al'aurar Fatima sai taga jini da maniyi a jikin ta, yayin da uwar taje dan taji ba'a si, sai mai laifin ya amsa laifin sa bai musa ba, daga haka sai suka kai kara gurin yan sanda.

An kama Johnson an kaishi ofishin yan sanda na unguwar Idumu, sashen binciken fyade da laifuka makamantan haka, shugaban hukumar ya shiga lamarin.

An dauki yarinyar aka kaita asibitin Rauf Arebegsola, inda ak bata kulawa a kyauta, har lokacin da ake ma yarinyar aiki akwai jini a maniyi a jikin ta, da farko dai mai laifin ya gudu, amma baban yarinyar tare da taimakon mahaifinta sun kama shi sun kai shi hannun yan sanda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lokacin da ake tabbatar da kama mai laifin da akayi, PPRO na yan sanda shiyar jahar Lagos Dolap Badmos tace kwamishinan yan sandan ya tabbatar da lamarin kuma aika da lamarin hannu sashen bincike na farin kaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng