Masari yana da hannu a matsalana - Tsohon gwamna Shema
Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema ya bayyana cewa kiyayya ce ya sa Gwamna Aminu Bello Masari ke neman tozarta shi bayan ya sa hukumar EFCC ta cafke shi bisa zargin almundahanar naira bilyan 74.6.
Shema ya nuna cewa a shirye yake ya kare kansa bisa zargin inda ya nuna rashin Jin dadinsa bisa Kalaman Masari wanda ya shawarce shi kan ya kare mutuncinsa a idon duniya.
Mai karatu zai iya tunawa cewa ajiya ne mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai na Gwamnan Katsina, Abdu Labaran ya ce kamata yayi tsohon gwamnan jihar Katsina Alhaji Ibrahim Shehu Shema ya ma gode ma Gwamna Masari a maimakon laifin sa da yake gani a cikin binciken nan da hukumar EFCC take yi masa don kuwa a cewar sa taimakon sa ne ma gwamna Masari yakeyi don ya fito fili ya kare kansa da martabar sa a bisa zarge-zargen da akeyi masa.
Mataimaki na musamman din ya ce kamata yayi Shema ya fito fili yanzu ya kare kansa ba wai ya rika ganin laifin Masari ba.
Abdu Labaran ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jihar inda yake mayar da martani a kan wata takardar da mai magana da yawun Ibrahim Shema din ya fitar a kwanakin baya.
A cikin sanarwar da shi Abdu Labaran din ya fitar ya ce: "Shawarar da zamu ba Shema shine na fito fili ya kare kansa kawai a gaban hukumomin da suke da alhakin bincikar sa ba wai ya rika yada labarai ba ba kan gado a shafukan jaridu da kuma kafar yada labarai ta zamani.
Asali: Legit.ng